Buhari ya rubuta wasika ga majalisar dattawa kan su tabbatar da Aishah Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan CBN

Buhari ya rubuta wasika ga majalisar dattawa kan su tabbatar da Aishah Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan CBN

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wasika ga majalisar dattawa, inda ya bukaci a tabbatar da Aishah Ahmad a matsayin mataimakiyar shugaban babban bankin kasa

- Ana sa ran misis Ahmad ta maye gurbin daya daga cikin mataimakan shugaban bankin Apex wanda yayi ritaya a wannan shekaran

- Shugaban kasar ya kuma bukaci a tabbatar da wasu 4 da aka zaba a matsayin mambobin kwamitin tsara kudi na CBN

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wasika ga majalisar dattawa a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba, inda ya bukaci mambobin majalisar masu rinjaye da su tabbatar da Aishah Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan babban bankin kasar, Premium Times ta ruwaito.

Fadar shugaban kasa ta sanar da zaban Misis Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan bankin apex a ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba.

NAIJ.com ta tattaro cewa Ike Ekweremadu, mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya bayyana cewa Aishah zata maye gurbin mataimakin gwamnan CBN wanda ya yi rtaya a farkon wannan shekara don aka akwai bukatar a tabbatar da ita.

KU KARANTA KUMA: Yan kunan bakin wake hudu sun mutu a wani hari mara nasara da suka kai Maiduguri

Shugaba Buhari ya kuma bukaci a tabbatar da wasu 4, Adeola Adenikinju, Aliyu Sanusi, Robert Asogwa da kuma Asheik Maiduguri a matsayin mambobin kwamitin shirya kudi na CBN.

Zasu maye gurbi mambobin kwamitin da wa’adinsu ya cika a wannan shekara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel