EFCC ta bankado Naira Biliyan 2.1 a asusun mahaifiyar uwargidan Jonathan

EFCC ta bankado Naira Biliyan 2.1 a asusun mahaifiyar uwargidan Jonathan

Hukumar EFCC ta bankado Naira Biliyan 2.114 a asusun bankin Magel Resort Limited, wanda wannan makudan kudi mallakin Misis Patience Jonathan da marigayiyar mahaifiyar ta Mama Charity Oba.

A cikin rahotannin da NAIJ.com ta samu da hukumar ta EFCC, yanzu jimillan kudi da bincike ya nuna cewa mallakin Patience ne sun tashi Naira Biliyan 17.

EFCC ta bankado Naira Biliyan 2.1 a asusun mahaifiyar uwargidan Jonathan

EFCC ta bankado Naira Biliyan 2.1 a asusun mahaifiyar uwargidan Jonathan

A makon da ya gabata ne uwargidan ta tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta shigar da karar cin zarafin ta da kuma dakile ma ta hakkin ta da hukumar ta EFCC ta ke yi, inda ta ce hukumar ta yi wada-wada da tunanin, muzguna ma ta tare da hana ta tsugono wanda har ya kai ga sanya katutu a asusun banki na mahaifiyarta.

KARANTA KUMA: Buhari ne ya bani damar aiki da Naira Biliyan 640 yayin da yake kasar Landan - Baru

Sakamakon haka ne Patience ta ke rokon kotu akan hukumar ta biya ta diyya har ta Naira Biliyan 2, wanda a yanzu hukumar ta na cigaba da tuhumar ta akan yin zamba na kudi wajen yin amfani da wasu kungiyoyi ma su zaman kansu.

Rahotanni daga hukumar sun bayyana cewa, akwai akalla Naira Biliyan 17 da suka shiga cikin asusun banki na kungiyoyi masu zaman kansu wanda mallakin Patience din ne.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel