Dalilanmu na goyon bayan haramta kungiyar IPOB - Ohanaeze Ndigbo

Dalilanmu na goyon bayan haramta kungiyar IPOB - Ohanaeze Ndigbo

- Ohanaeze Ndigbo ita ce kungiyar Kabilar Ibo zalla ta kasa

- Ta kunshi dattijanta na gargajiya da na siyasa

- Ta goyi baya gwamnoni da suka haramta kungiyar IPOB

Kungiyar dattijan kabilar Ibo ta kudancin Najeriya sun kare kansu daga samarin yankin na zargin su da cin amanar kasa, da yankan baya, ga kokarin samarin na ballewa daga Najeriya, da ma kafa tasu kasar ta kabilar Ibo mai suna Bayafra.

Dalilanmu na goyon bayan haramta kungiyar IPOB - Ohanaeze Ndigbo

Dalilanmu na goyon bayan haramta kungiyar IPOB - Ohanaeze Ndigbo

A sanarwar da suka fitar, ta bakin kakakinsu, sun ce ya kamata ne kabilar Ibo su dauka kishin bayafara a zuci yake, kuma nuna shi ta hanyar aiki tukuru da neman halas shi ya kamaci duk mai kishin kasarsa da kabilarsa.

A cewarsu dai, yayi wuri da za'a so a yanke cudanya da sauran kabilun kasarnan. Kuma ma wai ai kabilar ta Ibo ta zuba jari sosai a kasar nan don haka bai kamata ta gudu ta bar arzikinta ba.

'A jihar Legas kadai, kasuwanni fin goma muka kafa, kuma kowacce kasuwa na samar da naira biliyan akalla ukku a kowacce rana. Don haka, ba dabara bace a balle.'

DUBA WANNAN: Yara masu kiba na karuwa a duniya, bincike ya nuna

Su dai samarin yankin masu zafin kai na ganin dattijan basu yi musu adalci ba, a kokarinsu, tare da shugabansu Nnamdi Kanu, na sai sun kafa 'yantacciyar kasa mai cin gashin kanta, a gabashin kudancin Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel