Mu da muka sa hannu a takardun belin Nnamdi Kanu mun shiga uku - Abaribe

Mu da muka sa hannu a takardun belin Nnamdi Kanu mun shiga uku - Abaribe

Kafin a bada belin Nnamdi Kanu, sai da wasu dattijai suka yarda su mika kadarorinsu da sa hannunsu, a matsayin cewa shi dansu ne da ba zai zulle ba, amma sai gashi ya tsere ya barsu da afi.

Sanata Abaribe shine limamin kungiyar kabilar Ibo a cikin majalisar dattijai, kuma na kan gaba cikin wadanda suka tsayawa Nnamdi Kanu, kan lallai sai gwamnati ta bashi beli. Sai dai yanzu yana da-na-sanin tsayawa saurayin.

Mu da muka sa hannu a takardun belin Nnamdi Kanu mun shiga uku - Abaribe

Mu da muka sa hannu a takardun belin Nnamdi Kanu mun shiga uku - Abaribe

A cewar Abaribe dai, 'mu dukka da muka tsayawa Nnamdi Kanu, yanzu duk a tsure muke, mun mika sahalewarmu da sunanmu da kaddarorinmu, domin a samu a kubuto yaron nan, amma bamu ma san inda yake ba.'

Tun bayan shigar sojoji yankin na kabilar Ibo, inda suka dakushe kokarin samarin yankin na sai sun balle daga Najeriya, sai aka nemi Nnamdi Kanu aka rasa. Haka ma ranar da aka deba masa ta zuwa kotu a Abuja ta zo ta wuce ba'a ganshi ba.

DUBA WANNAN: An haramtawa likitoci yajin aiki, da ma hada aikin gwamnati da na waje

A wata majiya dai, tuni Nnamdi Kanu din ya shallake iyaka ya shiga kasar Kamaru, ya hau jirgi ya gudu Malaysia, daga nan ya wuce Indiya. A wata majiyar kuma, wai sojoji ne suka sace shi. Haka kuma, wasu ma na cewa ai tuni sojojin sun hallaka shi.

Gwamnati dai bata ce komai ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel