Ku binciki yaran ku don da yawa kwaya su ke sha – Inji Sanata Bruce

Ku binciki yaran ku don da yawa kwaya su ke sha – Inji Sanata Bruce

- Majalisar Dattawa za tayi bincike game da sha’anin shaye-shaye

- Sai dai wani Sanata yace Sanatocin su fara binciken daga gidajen su

- Sanata Ben Murray-Bruce yace da dama na yaran su ba su tsira ba

Sanatocin kasar nan sun ce dole ayi bincike game da yadda shan kayen maye ya zama ruwan dare a fadin kasar nan.

Ku binciki yaran ku don da yawa kwaya su ke sha – Inji Sanata Bruce

Sanata Ben Murray-Bruce yace Sanatoci su binciki yaran su

Sai dai wani Sanata na Jihar Bayelsa ya bayyana cewa kamata yayi abokan aikin na sa Sanatocin Kasar su fara wannan binciken daga gidajen. Sanatan yace mafi yawa daga cikin yaran da su ka haifa su na cikin masu shan kayan mayen.

KU KARANTA: Majalisa ta kira Shugaba Buhari ya sa kudi a harkar World Cup

A cewar Sanatan Matasa da dama ba su da aikin yi sai mugun shaye-shaye a Najerya inda yace abin da yake sa su zama cikin farin ciki kawai kenan. Fitaccen Sanatan Kasar ya bayyana wannan ne a shafin sa na Tuwita kamar yadda ya saba.

Wani bincike da Jaridar Daily Trust tayi ya nuna cewa daga Jihar Kano zuwa Jihar Jigawa ana shan akalla kwalabe miliyan 3 na maganin codeine a kowace rana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel