Matakan ministan shari'a ba zai sa mu dakatar da bincike IGP ba – Inji Majalisar Dattijai

Matakan ministan shari'a ba zai sa mu dakatar da bincike IGP ba – Inji Majalisar Dattijai

- Majalisar dattijai tace za ta ci gaba da bincike a kan IG na 'yan sanda

- Majalisar ta yanke shawarar bincike Idris a kan zargin da Misau ya yi masa game da cin hanci da rashawa

- Ana zargin hukumar 'yan sanda na Najeriya da Idris game da naira biliyan 120 daga ayyuka na tsaro

Majalisar dattijai ta jadadda shirye-shiryenta na ci gaba da gudanar da bincike kan zargin babban Sufeto na 'yan sanda, Mista Ibrahim Idris wanda sanata Isa Misau ya yi.

Shugaban kwamitin da’a na majalisar dattijai, Sam Anyanwu, ya shaidawa majiyar NAIJ.com cewa kwamitin za ta ci gaba da binciken tun da ba a shigar da ita cikin takardar da ministan shari'a da babban mai shari'a na tarayya suka gabatar a kan Misau a madadin IG na 'yan sanda.

Majalisar dattijai a ranar 4 ga Oktoba, 2017, ta yanke shawarar bincike Idris a kan zargin da Misau ya yi masa game da cin hanci da rashawa.

Zargin Misau ba zai sa mu dakatar da bincike IGP ba – Inji Majalisar Dattijai

Shugaban kwamitin da’a na majalisar dattijai, Sam Anyanwu

Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya umarci kwamitin da’a na majalisar don bincika abubuwan da yasa Misau ya yi ritaya daga hukumar 'yan sanda na Najeriya.

KU KARANTA: An zabi Namdas a matsayin mataimakin shugaban majalisar kasashen Afrika

Saraki ya kuma kafa wani kwamiti na musamman don bincike kan zargin da ake yi akan hukumar 'yan sanda na Najeriya da Idris game da naira biliyan 120 daga ayyuka na tsaro wanda ake karba a kowace shekara daga manyan mutane da kamfanoni masu zaman kansu a kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel