An nada Rahama Sadau mai gabatarwa a bikin gasar BON Awards ta bana

An nada Rahama Sadau mai gabatarwa a bikin gasar BON Awards ta bana

- Korarriyar jarumar nan ta Kannywood, Rahama Sadau ta samu karramawa na musamman

- Za’a gudanar da bikin ne a ranar Asabar, 16 ga Disamba, 2017 a garin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun

- Gwamnatin Jihar Ogun din ce ta dauki nauyin shirya bikin a wannan shekarar

Korarriyar jarumar nan ta Kannywood, Rahama Sadau ta samu karramawa na musamman, inda aka zabe ta a matsayin deaya daga cikin wadanda zasu yi aikin gabatarwa a gagarumin bikin karramawa na Nollywood wato shirin nan na Best of Nollywood Awards (BON) na wannan shekaran. Dayan shi ne wani fitaccen dan wasan kudu mai suna Gbenro Ajibade.

Za’a gudanar da bikin ne a ranar Asabar, 16 ga Disamba, 2017 a garin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Gwamnatin Jihar Ogun din ce ta dauki nauyin shirya bikin a wannan shekarar.

An nada Rahama Sadau mai gabatarwa a bikin gasar BON Awards ta bana

An nada Rahama Sadau mai gabatarwa a bikin gasar BON Awards ta bana

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Nnamdi Kanu yaki karrama yarjejeniyar da yayi da shugabannin Igbo - IPOB

A lokacin da ya ke magana da manema labarai kan zaben wadannan jarumai biyun, babban daraktan gasar ta BON, Mista Seun Oloketuyi, ya ce, “Zaben Rahama da Gbenro ya gudana ne bayan an bata hankalin dare sosai.

"Mun yi amfani da ka’idoji da su ka hada da tunanin saka mutane daga sassa daban-daban, kwarewa, da kuma yarinta; akwai wasu ’yan wasan wadanda mu ka lura da su, to amma dai Gbenro da Rahama ne su ka fi samun maki.

"Kuma a gaskiya mun yi murna da yadda su ka karbi gayyatar mu tare da nuna jin dadin su don shiga wannan abin tarihin.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel