Mun Gode – Inji Jama’an garin Gwoza ga Sojojin Najeriya (Bidiyo)

Mun Gode – Inji Jama’an garin Gwoza ga Sojojin Najeriya (Bidiyo)

Al’ummar garin Gwoza sun yi fitar farin dango, kwansu da kwarkwata kan babban titin garin Gwoza, suna wake sun shewa don taya Sojojin Najeriya murkushe yan ta’adda daga garin.

Kaakakin rundunar Sojin Najeriya Birdegiya SK Usman ne ya bayyana haka ta cikin wani faifan bidiyo daya daura a shafinsa na Facebook, kamar yaddda NAIJ.com ta gano.

KU KARANTA: Yaƙi da Boko Haram: Sojoji sun ƙwato makamai da motocin yaƙi na ýan ta’adda bayan sun kashe 15

An hangi mata, maza da kananan yara suna waka suna gudu, tare da shewa da annushuwa suna kiran ‘Winner! Karyansu’, yayin da wasu ke tafe akan kekekuna da babura.

Ga bidiyon a nan:

Suma Sojojin Najeriya ba’a barsu a baya ba, inda ake hange su suna tuka babura da manyan motoci, suna latsa oda, sa’annan aka hangi wasu suna atisaye akan titi, yayin da yara ke zagaye dasu suna yi musu waka.

A wani labarin kuma, rundunar Sojin Najeriya ta 192, Bataliya ta 26 na ‘Operation Lafiya Dole’ ta gwada kwanji da yan ta’addan kungiyar Boko Haram a ranar Talata 10 ga watan Oktoba.

Kaakakin rundunar ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda yace wannan gurmurzu ya faru ne da misalin karfe 8:35 na daren Talata, yayin da yan ta’addan suka kai samame a sasanin Sojoji dake Yamteke, karamar hukumar Gwoza.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Daga NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
'Yan Najeriya su na haukacewa a Kasar waje saboda wahala

'Yan Najeriya su na haukacewa a Kasar waje saboda wahala

'Yan Najeriya su na haukacewa a Kasar waje saboda wahala
NAIJ.com
Mailfire view pixel