Dalilin da yasa Nnamdi Kanu yaki karrama yarjejeniyar da yayi da shugabannin Igbo - IPOB

Dalilin da yasa Nnamdi Kanu yaki karrama yarjejeniyar da yayi da shugabannin Igbo - IPOB

- Kungiyar IPOB sun caccaki shugaban Ohameze Ndigbo

- Sun zarge shi da shirya makircin zama mataiamakin shugaban kasa a 2019

- Kungiyar tace zata cigaba da fafutukar Biyafara

Kungiyar masu fafutukar neman kafa yankin Biyafara (IPOB) sun soki Dr Nnia Nwodo, shugaban kungiyar datawan Igbo na Ohaneze Ndigbo cewa yana shirye-shiryen zamowa mataimakin shugaban kasa a 2019.

A wata sanarwa da aka saki a ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba, kungiyar tace ta rabe da shugaban Ohaneze Ndigbo sannan kuma cewa ya ji dacin rai saboda ba’a bari ya zamo shugaban yankin gabas ba.

Sun ce Kanu bai karrama yarjejeniya da sukayi da shugabannin Igbo a baya ba saboda dalilan su na son zuciya da kuma hadamar siyasa.

Kungiyar sun ce Nwodo na fushi saboda basu goyi bayan kudirinsa na son zama shugaban mutanen Igbo ba.

KU KARANTA KUMA: Rundunar Sojojin Najeriya ta karbe fadin Jihar Borno daga hannun 'Yan ta'adda

Kungiyar sun kuma yi zargin cewa Nwodo bai ji dadi a saboda ba’a bari ya halarci ganawar da Kanu yayi da shugabannin Igbo ba.

Sun kuma bayyana cewa lokacin da mataimakin shugaban kasa YeminOsinbajo ya kira wani zama tare da shugabannin Igbo Nwodo ya halarta ba tare da neman shawarar suba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel