Yaƙi da Boko Haram: Sojoji sun ƙwato makamai da motocin yaƙi na ýan ta’adda bayan sun kashe 15

Yaƙi da Boko Haram: Sojoji sun ƙwato makamai da motocin yaƙi na ýan ta’adda bayan sun kashe 15

Rundunar Sojin Najeriya ta 192, Bataliya ta 26 na ‘Operation Lafiya Dole’ ta gwada kwanji da yan ta’addan kungiyar Boko Haram a ranar Talata 10 ga watan Oktoba, kamar yadda NAIJ.com ta jiyo.

Kaakakin rundunar Sojin kasa, Birdegiya SK Usman ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda yace wannan gurmurzu ya faru ne da misalin karfe 8:35 na daren Talata, yayin da yan ta’addan suka kai samame a sasanin Sojoji dake Yamteke, karamar hukumar Gwoza.

KU KARANTA: Uwargidar Gwamnan jihar Katsina ta raba ma mata 1,000 naira 5,000,000

Yaƙi da Boko Haram: Sojoji sun ƙwato makamai da motocin yaƙi na ýan ta’adda bayan sun kashe 15

Motar Boko Haram

Sakamakon karfin makamai da Sojojin Najeriya ke da shi, sun samu nasarar yi ma yan ta’addan jini da majina, inda suka kashe yan ta’adda 15, tare da kwato tarin alburusai da bindigu da kuma motocin yaki masu dauke da bindigu akan su.

Bugu da kari sauran da suka sha daga cikin yan ta’ddan sun yi gudu tsira ne da raunukan da suka samu daga harbe harben da suka sha a hannun Sojoji.

Yaƙi da Boko Haram: Sojoji sun ƙwato makamai da motocin yaƙi na ýan ta’adda bayan sun kashe 15

Yaƙi da Boko Haram

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa an ji ma wani Sojan Najeriya guda daya rauni a sanadiyyar musayar wutan da aka yi da yan ta’addan.

Yaƙi da Boko Haram: Sojoji sun ƙwato makamai da motocin yaƙi na ýan ta’adda bayan sun kashe 15

Motar yaki

Daga karshe, SK Usman ya bada tabbacin kokarin Sojojin Najeriya na cigaba da bada tsaro ga dukiya da rayukan al’umma, sa’annan ya bukaci jama’a dasu cigaba da baiwa Sojoji muhimman bayanai don samun daman kawar da barazanar Boko Haram.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel