Ra'ayoyin 'yan Arewa game da yi wa kasa garanbawul sun banbanta

Ra'ayoyin 'yan Arewa game da yi wa kasa garanbawul sun banbanta

- Atiku ya nace kan bayar da karfin iko da albarkatun kasa zuwa hannun Jihohi

- Ango Abdullahi ya ce a koma tsarin yankunan Arewa da Kudu na 1914

- El-Rufa'i na da fahimtar za'a magance matsaloli idan Gwamnati ta sauke nauyin da ya rataya a wuyar ta

A jiya ne shuwagabanni da kungiyoyin Arewa su ka bayyana ra'ayoyi mabambanta game da yi wa kasa garanbawul a wani taron kwana 2 da Kungiyar Bincike da Cigaban Arewa wato ARDP ta shirya a Kaduna.

A taron mai taken, ''Arewa da Kasar Najeriyar Gobe'', Aminu Tambuwal ya karyata zancen da ke cewa Arewa ba ta goyon garanbawul din. Sai dai ya ce dole ne sai an zauna an tsara yadda za'a bullowa lamarin. Kuma dole a zurfafa tunani akan sakamakon da shawarwari da ra'ayoyi za su haifar.

Ra'ayoyin 'yan Arewa game da yi wa kasa garanbawul sun banbanta

Ra'ayoyin 'yan Arewa game da yi wa kasa garanbawul sun banbanta

Shi kuwa Atiku Abubakar ta bakin wakilin sa, ya na nan kan bakan sa na mayar da karfin iko na zartar da al'amurra zuwa hannun jihohi, a inda za'a bar habaka tattalin arzikin kasa a hannun Gwamnatin Tarayya. Ya kuma ce Arewa bata da abun tsorata game da garanbawul saboda tana da yawan jama'a da albarkatu, hasali ma, man fetur ya kusa zama tarihi.

DUBA WANNAN: Biyafara: An dage sauraron Shari'a tsakanin Nnamdi Kanu da Gwamnatin Tarayya

Ango Abdullahi kuwa cewa ya yi babu garanbawul din da ya wuce komawa asalin yadda Najeriya ta ke na kasancewa yankin Arewa da na Kudu a 1914. Ya ce wannan tarayya na Kasa daya ta fi cutar da Arewa bisa sauran yankunan. Ya kuma ce ba'a jin iface-iface sai lokacin da dan Arewa ke mulki.

Nasiru El-Rufa'i na da fahimtar za'a shawo kan lamarin ne idan Gwamnati ta iya sauke nauyin talaka da ya rataya a wuyar ta. Ya ce ya kamata a mayar da hankaki wurin magance talauci da jahilci da rashin tsaro a kasar.

Kungiyoyin Jama'atu (JNI) dana Kiristoci (CAN) na Arewa, sun ce kasancewa Kasa shi ya fi. Ita kuwa Jam'iyyar Matan Arewa cewa ta yi magance rikicin yi wa kasa garanbawul ba zai magance rikicin shugabanci ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel