Wata kungiya tayi kira ga shugaba Buhari ya canja Aisha Ahmad

Wata kungiya tayi kira ga shugaba Buhari ya canja Aisha Ahmad

- Wata kungiya ta yi kira ga Buhari da ya canja mataimakiyar shugaban bankin Najeriya wato CBN

- Kungiyar ta ce Aisha Ahmad bata cancanta ta zama mataimakiyar shugaban ba

- Kungiyar ta ce wadanda suka bijiro ta ga Bubari ba su ba Buhari cikakken bayanin ta ba

Wata kungiyar Tabbatar da adalci ta yi kira ga Buhari da ya canja mataimakiyar shugaban bankin CBN don a cewar kungiyar, Aisha Ahmad bata cancanta ba.

Daraktar Kungiyar mai suna Mary Ogwiji ce ta yi wannan kira yayin zantawa da manema labarai jiya a Abuja. Mary ta kuma ce nadin Aisha a irn wannan lokaci da kasar ke bukatan kwararru a fannin tattalin arziki, abun takaici ne.

Wata kungiya tayi kira ga shugaba Buhari ya canja Aisha Ahmad

Wata kungiya tayi kira ga shugaba Buhari ya canja Aisha Ahmad

Ta ce nadin nata ba komai bane sai yunkurin da wasu ke yi na kawo cikas ga kokarin da Buhari ke yi na saita kasan nan. Ta kuma ce suna sane da cewar ba'a yi wa Buhari cikakken bayanin Aisha ba.

DUBA WANNAN: Buhari yaci amanar musulmai bisa nadin Aisha Ahmad a CBN

Kungiyar ta kuma ce ba'a bayyana wa Buhari cewan akwai wasu a sauran yankunan kasar da suka fi Aisha cancantar rike mukamin ba. Don haka zaban Aisha koma bayan su na nuna tsabar son kai da kabilanci da wariya.

Ba da dadewa ba naij.com ta kawo maku yadda wani ya koka da nadin Aisha yana mai cewa nadin nata cin fuska ne ga Musulmin Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel