Boko Haram: Rundunar Sojin Najeriya ta kashe ‘Yan ta’adda rututu

Boko Haram: Rundunar Sojin Najeriya ta kashe ‘Yan ta’adda rututu

- Rundunar Sojin Najeriya ta kashe ‘Yan ta’adda 40 a Dajin Sambisa

- Sojojin Kasar sun kuma damke ‘Yan ta’addan kusan su 18 a Dajin

- Haka kuma an ceto Bayin Allah sama da 200 a cikin wannan jiya

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana nasaorin da su ka samu hannun Boko Haram a Dajin Sambisa a cikin watan da ya gabata.

Boko Haram: Rundunar Sojin Najeriya ta kashe ‘Yan ta’adda rututu

Rundunar Sojin Operation Lafiya Dole

Mun samu labari daga Information Nigeria cewa Rundunar Sojin Najeriya ta kashe ‘Yan ta’addan Boko Haram har 40 a cikin Dajin Sambisa a watan da ya wuce. Haka kuma Sojojin Kasar sun kuma damke ‘Yan ta’addan har su 18 a Dajin na Sambisa.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun karbe makaman yaki daga Boko Haram

Shugaban Rundunar Operation Lafiya Dole Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya bayyana wannan a zantawar da yayi da ‘Yan Jarida a jiya Laraba. Janar Attahiru yace Sojojin sa sun ceto mutane 230 daga hannun ‘Yan Boko Haram a watan jiya.

Cikin wadanda aka hallaka akwai manyan ‘Yan Boko Haram Abdu Kawuri and Abubakar Benishek da wani Ba’abba Ibrahim. Dama can kun ji irin galabar da Sojojin Kasar su ka samu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel