A jefa kudin da aka samu daga barayi wajen Gasar cin kofin kwallon kafa - Inji Sanatoci

A jefa kudin da aka samu daga barayi wajen Gasar cin kofin kwallon kafa - Inji Sanatoci

- Majalisar Dattawa tace dole a marawa Super Eagles baya

- Najeriya ta samu zuwa Gasar cin kofin Duniya na badi

- Sanatocin kasar sun ce dole a ba harkar kwallo muhimmaci

Majalisa ta kira Shugaba Buhari ya sa kudi wajen ganin Najeriya ta yi kokari a Gasar cin kofin Duniya watau world cup da za ayi a shekara mai zuwa a Kasar Rasha.

A jefa kudin da aka samu daga barayi wajen Gasar cin kofin kwallon kafa - Inji Sanatoci

A ba Gasar World Cup muhimmanci Inji Sanatoci

Sanatocin Najeriya sun kira Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi amfani da wasu daga kudin da aka karbe hannun barayin Gwamnati wajen habaka harkar Gasar kwallon kafa domin ganin Najeriya ta tabuka abin kirki a Gasar na Duniya da za ayi a 2018.

KU KARANTA: Tsohon Kyaftin din Super Eagles ya bar tarihi

Majalisar Dattawan tace dole a marawa 'Yan wasan kasar baya wajen ganin sun tabuka abin kirki a Gasar mai zuwa ba kurum iyakar kokarin da aka yi ba kenan. Sanata Obinna Ogba wanda shine Shugaban kwamitin harkokin wasan kwallon kafa yace sai Gwamnati ta kara kaimi.

Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki ya goyi bayan haka inda ya kuma gargadi Hukumar kwallon kafa ta kasar NFF da barnatar da kudin Hukumar FIFA na kwallon kafa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel