Rundunar Sojojin Najeriya ta karbe fadin Jihar Borno daga hannun 'Yan ta'adda

Rundunar Sojojin Najeriya ta karbe fadin Jihar Borno daga hannun 'Yan ta'adda

- Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasara kan 'Yan Boko Haram

- Sojojin Operation lafiya dole sun karbe Borno daga hannun ta'adda

- Janar Ibrahim Attahiru yayi wannan cika-bakin kwanan nan

Mun samu labari daga filin daga cewa Sojojin Najeriya sun samu babbar galaba a kan 'Yan ta'addan Boko Haram a Garin Borno.

Rundunar Sojojin Najeriya ta karbe fadin Jihar Borno daga hannun 'Yan ta'adda

Shugaban wata Rundunar Sojin kasar Janar Attahiru

Sojojin Najeriya sun tabbatar da cewa sun karbe kaf fadin Jihar Borno daga hannun 'Yan ta'addan Boko Haram. Shugaban Rundunar Sojojin Operation lafiya dole Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya bayyana wannan da bakin sa inda yace kwanan nan ba da jimawa ba za a manta da wasu 'Yan Boko Haram.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya taya wani Dan Borno murna

A cewar Janar Attahiru a halin yanzu babu wani Karamar Hukumar Jihar ta Borno ko daya a hannun 'Yan Kungiyar Boko Haram. Janar din yace Sojojin Operation lafiya dole sun tarwatsa 'Yan ta'adda a hare-haren da aka rika kai masu ta sama da kasa.

Sojojin dai sun fara aika Rundunar Operation deep punch wanda bayan nan kuma aka saki Operation Ruwan wuta wajen ganin bayan 'Yan ta'addan. Yanzu dai ana kokarin ganin wadanda je gudun hijira sun koma Garuruwan su ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel