2019: Kungiyar matasan PDP ta amince da David Mark a matsayin dan takarar shugaban kasa

2019: Kungiyar matasan PDP ta amince da David Mark a matsayin dan takarar shugaban kasa

- Kungiyar matasan jam'iyyar PDP ta amince da David Mark a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2019

- Kungiyar ta ce ta kammala shirye-shirye na yakin neman zabe wanda za a gudanar a Sakkwato, karshen makon nan

- Ali Kano ya ce an shirya taron ne don neman goyon baya ga shugabancin Mark

Kungiyar matasan jam'iyyar adawa ta PDP ta amince da tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark ya tsaya takarar neman shugaban kasa a zaben shekara ta 2019.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, kungiyar ta bayyana hakan a ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba, cewa ta kammala shirye-shirye na yakin neman zabe wanda za a gudanar a Sakkwato, a karshen makon nan don bashi goyon baya.

Mai gudanar da harkokin kungiyar na kasa, Alhaji Abdullahi Ali Kano, ya shaida wa wakilinmu cewa, an shirya taron ne don neman goyon baya ga shugabancin Mark.

2019: Kungiyar matasan PDP ta amince da David Mark a matsayin dan takarar shugaban kasa

Tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark

Ali Kano, wanda ya kasance mamba na kwamitin yakin neman zabe a jam'iyyar PDP a zaben shekata ta 2015, kuma wakili a taro na kasa wanda aka gudanar a 2014, ya ce Mark yana da dukkan halaye da ake bukata a matsayin shugaba.

KU KARANTA: An zabi Namdas a matsayin mataimakin shugaban majalisar kasashen Afrika

"Mark bai taba barin jam’iyyar PDP ba, tun lokacin da aka kafa ta. Shekaru 19 yanzu haka, ya kasance mai aminci da kuma biyayya ga jam'iyyar. Ya nuna cewa shi cikakken dan siyasa ne", in ji Ali Kano.

Ya ce za a gudanar da taron a duk jihohi 36 na kasar, ciki har da birnin tarayya ta Abuja (FCT).

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel