Sakkwato: Makiya ba za su iya sa ni fada da Tambuwal ba – Inji Wamakko

Sakkwato: Makiya ba za su iya sa ni fada da Tambuwal ba – Inji Wamakko

- Tsohon gwamnan jihar Sakkwato ya ce makiya ba za su iya hada shi da gwamna Tambuwal ba

- Sanata Wamakko ya ce shi da gwamnan jihar Sakkwato daya ne

- Sanatan ya bayyana cewa babu wani abu tsakaninsa da Tambuwal sai mutunta juna da ƙauna ga juna

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko, ya gargadi wadanda ya ce suna kokarin yunkurin kula makirci don jawo baraka tsakaninsa da magajinsa, Aminu Tambuwal.

"Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da ni daya ne, kuma bakin mu daya, wanda ta saba wa makirce-makircen wasu masu jita-jita”, Wamakko, wanda ke wakiltar mazabar Sakkwato ta arewa ya ce.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari game da sanarwar da mataimakin na musamman a kan labarai da hulda da jama’a, Bashir Rabe Mani ya sanya, ya ce, sanata Wamakko ya yi magana a gidansa na Gawon Nama a Sakkwato, lokacin da yake jawabi ga babban taron jama'a wanda suka yi masa maraba daga filin jirgin sama na Sultan Abubakar III, Sakkwato, lokacin da ya dawo daga Abuja.

Sakkwato: Makiya ba za su iya sa ni fada da Tambuwal ba – Inji Wamakko

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko

"Ni da gwamna Aminu Tambuwal daya ne kuma muna da hangen nesa da manufa daya", in ji shi.

KU KARANTA: A jefa kudin da aka samu daga barayi wajen Gasar cin kofin kwallon kafa - Inji Sanatoci

Sanata Wamakko, ya sake jaddada cewa, "Babu wani abu tsakanin mu sai mutunta juna da ƙauna ga juna, da kuma ƙaunar jihar mu da Najeriya baki ɗaya".

"Gwamnan kuma dan’uwana yana girmama ni sosai. Ina mai godiya ga wannan, kuma ina kaunar ayyukansa", inji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel