Yankin arewa a shirye yake koda Najeriya zata rabe - Ango Abdullahi

Yankin arewa a shirye yake koda Najeriya zata rabe - Ango Abdullahi

Tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, Farfesa Ango Abdullahi, ya bayyana cewar yankin arewacin Najeriya a shirye yake tsaf koda Najeriya zata rabe. Ango ya ce arewa ta shirye take ta koma kan tsarin 1914 kafin a kirkiri gamammiyar Najeriya.

Dattijon ya bayyana abinda yake ran sa ne a wani taron kwana biyu da aka gudanar a kan nazarin bunkasa yankin arewa, karkashin kungiyar "Arewa Research Development Project (ARDP)".

"Idan ba zamu iya komawa tsarin shekarar 1914 ba, to mu koma tsarin shekarar 1960 na gwamnatin shiyya. Arewa bata tsoron komawa kamar yadda mu ke kafin a hade mu a matsayin kasa guda". A jawabin Ango Abdullahi.

Yankin arewa a shirye yake koda Najeriya zata rabe - Ango Abdullahi

Farfesa Ango Abdullahi

Farfesa Ango ya bayyana cewar matukar ana so a canja fasalin Najeriya to a koma ta inda aka fara, ko wanne yanki ya koma matsayin sa kafin kirkirar gamammiyar Najeriya. Ya kara da cewar Najeriya nada jihohi 36 da suka samu daga kowacce shiyya ta Najeriya amma har yanzu mun rasa samun hadin kai duk da yawan canje-canje da aka yiwa kundin tsarin mulki. A saboda haka ya kamata mu gane cewar ba zamu hadin kai ba musamman ganin yadda ko wanne yankin ke tayar da husuma matukar ba nashi ne ke mulkin kasa ba.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya taya Zanna Mustapha murnar cin lambar yabo na kungiyar UNHCR

Farfesa Ango ya ce arewa ce ta fi shan wahala a hannun mutanen kudu duk lokacin da ya kasance dan arewa ke shugabancin kasa kuma duk lokacin da aka yi maganar hadin kan Najeriya, arewa ke yin rawar gani tare da sadukarwa domin 'yan arewa ne suka fi son zaman lafiya tun farkon kafa Najeriya.

Ango ya ce tun daga batun kama-kamar mulki tsakanin kudu da arewacin Najeriya ya kamata jama'a su gane cewar babu maganar gamammiyar Najeriya, duk yaudarar kai ce kawai, don haka gara ma mu rabu kowane yanki ya kafa gwamnatin sa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel