An zabi Namdas a matsayin mataimakin shugaban majalisar kasashen Afrika

An zabi Namdas a matsayin mataimakin shugaban majalisar kasashen Afrika

- Hon. Abdulrazak Namdas ya ci zabe a matsayin mataimakin shugaban majalisar kasashen Afrika

- A ranar Talata aka zabi Namdas a kasar Afrika ta kudu a zaman majalisar

- Kakakin majalisar wakilan Najeriya ya taya Namdas murna

Dan majakisar wakilai, Hon. Abdulrazak Namdas (APC, Adamawa) kuma shugaban kwamitin watsa labarai da harkokin hulda da jama'a na majalisar wakilai an zabe shi a matsayin mataimakin shugaban majalisar kasashen Afrika.

NAIJ.com ta tattaro cewa, an gudanar da zaben a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba a zaman majalisar wanda aka yi a Afirka ta Kudu.

Kamar yadda mai magana da yawun shugaban majalisar wakilan Najeriya, Turaki Hassan ya sanar a madadin Namdas, dan majalisar kasar Ghana, Hon. Mohammed Muttaka ne ya gabatar da shi, kuma daga bisani ‘yan majalisar yankin kasashen yammacin Afrika suka zabe shi gaba daya.

An zabi Namdas a matsayin mataimakin shugaban majalisar kasashen Afrika

Dan majakisar wakilai, Hon. Abdulrazak Namdas (APC), Adamawa

Da wannan ci gaban, Hon. Namdas ya shiga cikin shugabannin majalisar kasashen Afrika.

KU KARANTA: Sunaye 17 dake nuna alakar kabilancin Buhari da Jonathan wajen nade-nade a kamfanin NNPC

Yayin da yake sanar da ci gaban a zauren majalisa a ranar Laraba, kakakin majalisa Yakubu Dogara, ya taya Namdas murna a matsayin mataimakin shugaban majalisar kasashen Afrika shiyar Afrika ta yamma.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel