Arewa ne zata fitar da Shugaban Kasa a 2019 - Orji Kalu

Arewa ne zata fitar da Shugaban Kasa a 2019 - Orji Kalu

- Dakta Orji Uzor kalu ne ya fadi hakan a ranar Labara

- Ya ce sauran yankuna sai suyi hakuri su jira zuwan 2023

- Ya kuma ce ko wace yanki tana da matsalar da take fuskanta, ba IPOB kadai bace a ke nuna wa wariya

Tsohon Gwaman Jihar Abia wato Orji Uzor Kalu, ya ce dole a kyale Arewa ta cikasa sauran shekarun ta 4 na shekaru 8 a kujerar Shugabancin Kasa. Ya ce dole sauran yankunan su hakura har sai 2023.

Ya yi wannan bayani jiya ga manema labarai bayan kammala wata tattaunawar sirri da ya yi tare da tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Babangida, a gidan sa na kan tsauni da ke Minna. Ya ce lallai dan Arewa ne zai fito takarar Shugabancin kasa koda kuwa Buhari ba zai fito ba.

Dole Arewa ta fitar da Shugaban Kasa a 2019 - Orji Kalu

Dole Arewa ta fitar da Shugaban Kasa a 2019 - Orji Kalu

A cewar sa duk da shi ma yana da ikon fitowa takarar, amma yana kan fahimtar wannan lokaci ne na Arewa. Ya ce adalci yana da matukar muhimmanci don haka dole Arewa ta cikasa shekarun ta.

DUBA WANNAN: Ibo su hakura da Biyafara, in ji Enamhe

A game da wariya da wasu yankuna suke kukan ana masu, musamman yankin Kudu masu Gabas, kalu cewa 'yan kabilar Ibo ba su kadai bane ake nuna wa waiya. Ya ce ko wace yanki tana da nata matsalar da take fuskanta.

Kalu ya ce rashin adalci da sauke nauyin Gwamnati kan al'umma shi ke janyo dukkan hatsaniya a kasar. Don haka daukacin talakawa ake wa wariya ba IPOB kawai ba. Ya ce IPOB tana da ikon fafutukar ta amma bata da ikon neman raba kasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel