Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi tayi ram da masu saafarar kwayoyi su 19 a Legas

Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi tayi ram da masu saafarar kwayoyi su 19 a Legas

Hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama wasu mutane su 19 dauke da haramtattun kwayoyi kilo 14.30 a filin jirgin jihar Legas.

Hukumar ta bayyana haka ne ta bakin Kaakakin ta, Jonah Achema a ranar Laraba 11 ga watan Oktoba, inda yace sun kama mutanen ne cikin wata 3 da suka gabata, inji rahoton Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Labaran Kannywood: An karrama jaruman Kannywood da kyautuka a Abuja

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito kwayoyin da aka kama sun hada da kilo 2.575 na hodar iblis, kilo 5.100 na tabar wiwi, da sauran kwayoyi nau’i daban daban.

Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi tayi ram da masu saafarar kwayoyi su 19 a Legas

NDLEA

Jonah ya tabbatar da cewa a yanzu haka suna bincikar wasu jami’ansu dake da hannu cikin shigo da muggan kwayoyi, kuma har sun gurfanar dasu gaban kotu, sa’annan yace ba zasu kyale wani shafaffe da mai ba a hukumar.

“Muna tabbatar ma jama’a cewa ba zamu kare duk wani jami’in mu da muka kama da laifi ba, amma fa ba zamu yi aiki da zargin shaci fadi ba.”

Daga karshe ya jadda manufar hukumar na aiki kafada da kafada da yan jaridu wajen yin aikinsu yadda ya kamata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel