Ibo su hakura da Biyafara, in ji Enamhe

Ibo su hakura da Biyafara, in ji Enamhe

- Marc Enamhe ya yi kira ga Ibo da su hakura da fafutukar kafa Biyafara

- Ya ce fafutukar ta su bata wuce neman jan ragamar mulkin Najeriya

- Ya kuma ce 'yan kabilar igbo su na da girman kai wanda ke tsorata 'yan Najeriya

Tsohon ciyaman na Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) Barista Marc Enamhe ya yi kira ga 'yan kabilar Ibo da su hakura da fafutukar neman kafa kasar Biyafara saboda yadda take kwaranyewa tsakanin su da sauran 'yan Najeriya.

Yayin ganawa da jaridar Daily Post, Marc ya yi kira ga Ibo da su zamo masu saukin kai kamar yadda hausawa su ke. Ya ce ba laifi bane yin fafutukar amma ya kamata a ce Ibo sun wadata da daukakan da su ke da shi.

Ibo su hakura da Biyafara, in ji Enamhe

Ibo su hakura da Biyafara, in ji Enamhe

Ya cigaba da cewa ko su na da kasar kan su ko ba su da shi, su mutane ne masu daukaka. Ya kuma ce fafutukar ta su bata wuce neman jan ragamar mulki Najeriya wanda hakan zai yi wuya saboda girman kan su na tsoratar da 'yan Najeriya.

DUBA WANNAN: Biyafara: An dage sauraron Shari'a tsakanin Nnamdi Kanu da Gwamnatin Tarayya

Ya jawo hankalin su da su zauna su yi karatun ta-natsu don fahimtar dalilin da yasa basu samun nasara duk lokacin da su ka nemi a ware. A cewar sa, ya kamata su wadatu da kasancewar su shahararrun 'yan kasuwa. Inda sun lura, wanda suka fi kowa kudi a duniya 'yan kasuwa ne ba ma'aikatan Gwamnati ba.

Ya ce su na bukatan sauran 'yan Najeriya kamar yadda su ma sauran 'yan Najeriya ke bukatar su. Ya kara da cewa tattalin arzikin Najeriya ya na bukatar gwanancewar su kan harkan kasuwan ci.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Soyayyar Maryam Yahaya da wani furodusa ta fito fili

Dandalin Kannywood: Soyayyar Maryam Yahaya da wani furodusa ta fito fili

Dandalin Kannywood: Soyayyar Maryam Yahaya da wani furodusa ta fito fili
NAIJ.com
Mailfire view pixel