Gwamnati ta biya diyyar asarar da gudanarwar soji ta janyo - Makusantan Kanu

Gwamnati ta biya diyyar asarar da gudanarwar soji ta janyo - Makusantan Kanu

Dangin Mazi Nnamdi Kanu wanda shine shugaban masu fafutikar neman kafa yankin Biyafara, su na kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya aka tayi azamar biyan su diyya dangane da asarar dukiya wanda gudunarwa sojin kasa ta yi sanadi yayin aiwatar da aikace-aikacen ta a yankin Afaraukwu Ibeku dake karamar hukumar Arewacin Umuahia a jihar Abia.

Wannan bukata ta zo ne a rubuce da sa hannun shugaban kungiyar unguwanni Cif Ikechukwu Ndubueze da sakataren kungiyar Honarabul Ikechukwu Chiabuotu tare da sauran wakilan wasu kauyuka da suka hadar da; Ugochukwu Iroegbu mai wakilcin Etitinabu, Jude Ekwuribe mai wakilcin Ndagbo, Nze Ifeanyi Nwaubani mai wakilcin Mgboko da Ojimndu Iroegbu mai wakilcin Omuobasi, inda suka bayyana irin asarar da gudanarwar Python Dance II ta dakarun soji ta janyo a yankunan.

Gwamnati ta biya diyyar asarar da gudanarwar soji ta janyo - Makusantan Kanu

Gwamnati ta biya diyyar asarar da gudanarwar soji ta janyo - Makusantan Kanu

A cewarsu, gudanarwar dakarun sojin kasan ta yi sanadiyar salwantar rayuka, asarar dukiya da muhallai, bacewar mutane da dama wanda ya hadar da har basaraken su na gargajiya Eze Israel Kanu wanda shine mahaifin Kanu da kuma mai dakinsa Sally, baya ga tsaiko da gudanawar ta janyowa harkokinsu na kasuwanci.

A yayin da suke zayyano bukatunsu ga gwamnatin na biyansu diyya, al'ummar Afaraukwu kuma su na tuhumar dakarun sojin da aiwatar da gudanarwarsu kan cewa ta zarce ka'idar kundin tsari na kasa wajen dakile hakkin masu tayar da kayar baya cikin lumana na fafutikar neman kafa yankin Biyafara.

KARANTA KUMA: Buhari ne ya bani damar aiki da Naira Biliyan 640 yayin da yake kasar Landan - Baru

"Ba bu wani mahaluki da zai yi ikirarin ya yi idanu biyu da bindigar Ak 47 a wurin masu fafutikar neman kafa yankin Biyafara na yankunan Kudu maso gabas kamar yadda makiyaya ke yi, kuma ba a taba jin mu da harbe-harbe ba ko tayar da wata tarzoma ko hasumiya".

"Saboda haka wannan gudanarwar da dakarun soji ke yi ba ta cikin tsarin demokuradiyya".

Kungiyar ta na kuma janyo hankalin al'ummar Najeriya, akan irin yaudarar da shugaban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi, wajen cewar wai gudanarwar su ta Python Dance II ta zo ne domin kawokarshen duk wani ta'addanci a kasar nan baki daya.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel