Uwargidar Gwamnan jihar Katsina ta raba ma mata 1,000 naira 5,000,000

Uwargidar Gwamnan jihar Katsina ta raba ma mata 1,000 naira 5,000,000

Matar gwamnan jihar Katsina Hajiya Zakiyya Masari ta raba ma matan karkara su dubu daya, naira miliyan biyar a matsayin tallafi ga, kamar yadda kamfanin dillancin labaru ta ruwaito.

Kaakakin Uwargidar gwamnan Hajiya Hauwa Jikamshi ta shaida ma majiyar NAIJ.com a ranar Laraba cewar an raba tallafin ne a kananan hukumomin Ingawa, Baure da Sandamu.

KU KARANTA: Alheri gadon barci: Sarkin Gombe ya samar ma matasa 28 aikin Soja da Ɗansanda (Hotuna)

Jikamshi tace kowanne daga cikin matan ta samu N,5000 da kuma kayan abinci kamar su garin Fulawa, taliya da sauran kayyakin tallafi, haka nan tace an raba wannan kayan tallafi ne da nufin bunkasa karfin arzikin matan, tare da inganta rayukansu.

Uwargidar Gwamnan jihar Katsina ta raba ma mata 1,000 naira 5,000,000

Uwargidar Gwamnan jihar Katsina

A wani labarin kuma, Uwargidar gwamnan ta baiwa masu cutar sikila magunguna kyauta a asibitin Ingawa, don saukaka musu radadin ciwon.

Daga karshe Jikamshi ta nanata manufar uwargidar gwamnan na inganta rayuwar mata da matasan jihar Katsina, gaba daya. a kwanakin baya ma Uwargidar gwamnan ta baiwa mata a karamar hukumar Daura, Maiadua da Mani irin wannan tallafi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel