Shugaba Buhari ya taya Zanna Mustapha murnar cin lambar yabo na kungiyar UNHCR

Shugaba Buhari ya taya Zanna Mustapha murnar cin lambar yabo na kungiyar UNHCR

- Shugaba Buhari ya taya dan Najeriya Zanna Mustapha murna bisa samun lamabar yabo

- Shugaban yace Zanna ya sami lambar yabon ne bisa sadaukar da kai da taimakawa yan sansanin gudun hijira

- Shugaba Buhari yayai kira ga sauran yan Najeriya da suyi amfani da baiwar da Allah ya basu domin taimakawa wadanda ke bukatar taimakon

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murna ga wani dan Najeriya mai suna Zannah Mustapha bisa nasarar samun lambar yabo na majalisar dinkin duniya (UNHCR) bisa taimakon 'yan gudun hijira da yayi a shekarar 2017.

A madadin 'yan Najeriya baki daya, shugaba Buhari yana taya Mustapha murnar samun lambar yabon domin nuna hazaka a fanin ilimi, samar da zaman lafiya da yin sulhu a yankin Arewa maso Gabashin najeriya ta hannun mai taimaka masa wajen hulda da jama'a Femi Adesina.

Shugaba Buhari ya taya dan Najeriya da ya sami lambar yabo murna

Shugaba Buhari ya taya dan Najeriya da ya sami lambar yabo murna

Shugaba Buhari yayi ammana cewa Mustapha ya samu lambar yabon ne saboda jarumtakar sa, aiki tukuru da sadaukarwar sa a sansanin yan gudun hijira duk da cewa wani lokaci yana jefa rayuwar sa cikin hadari.

DUBA WANNAN: Biyafara: An dage sauraron Shari'a tsakanin Nnamdi Kanu da Gwamnatin Tarayya

Shugaba Buhari yayi kira ga yan Najeriya baki daya da suyi koyi da irin halaye na gari na Mustapha wurin amfani da baiwar da Allah (SWT) ya basu domin taimkawa wa wanda suke cikin fitina.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel