Mu na tantamar yadda ake gudanar da shari'ar 'yan Boko Haram a sirrance - Kungiyar Amnesty International

Mu na tantamar yadda ake gudanar da shari'ar 'yan Boko Haram a sirrance - Kungiyar Amnesty International

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana damuwar ta a ranar Laraba 11 ga watan Oktoba, kan yadda ake gudanar da shari'ar 'yan ta'addan Boko Haram ba a bainar al'umma ba da kuma manema labarai wai don daukan matakan tsaro.

Shari'ar da aka fara gudanarwa a cikin wannan mako a wasu kotun farar hula guda hudu da aka kafa barikin dakarun soji dake garin Kainji a jihar Neja,inda 'yan ta'addan da ake zargi guda 1, 669 suka gurfana a gaban alkalai.

Gwamnati ta bayyana cewa akwai 'yan ta'adda 651 dake tsare a yankin Arewa maso Gabas na birnin Maiduguri, wanda su ma za a fara gudanar da ta su shari'ar da zarar an kammala wacce ke gudana a garin Kainji.

Mu na tantamar yadda ake gudanar da shari'ar 'yan Boko Haram a sirrance - Kungiyar Amnesty International

Mu na tantamar yadda ake gudanar da shari'ar 'yan Boko Haram a sirrance - Kungiyar Amnesty International

Shugaban kungiyar ta Amnesty reshen Najeriya Osai Ojigho, ya bayyana cewa ya kamata wannan shari'a ta baiwa wadanda ta'addancin Boko Haram din ya zalunta damar jin danshin adalci a tattare da su idan har za agudanar da shari'ar a bayyane.

Ya ke cewa, "yadda ake gudanar da shari'ar nan a sirrance ba tare da bayyana ta ga manema labarai da kuma al'umma ba yana matukar janyo tantama da kuma damuwa acikin al'umma.

KARANTA KUMA: Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadin rai 1 tare da jigata 19 a jihar Legas

"Gudanar da shari'a a bainar al'umma ya kare hakkin dan Adam wajen samun yin adalci a shari'ar".

A yayin haka dai, kungiyoyin kare hakki da dama su na tuhumar sojin Najeriya da kama dubunnan mutane farar hula ba bisa ka'ida ba tun da wannan rikici na Boko Haram ya kunno kai a shekarar 2009.

Da yawan wannan mutane su na tsare ne shekara da shekaru cikin cinkoso da rashin kwanciyar hankali tare da rashin basu damar gurfana a gaban kotu.

Ojigho ya kara da cewa, kotu ta gaggawar sakin wadanda aka tsare a Kainji idan har ba ta samu kwararan dalilai da hujjoji akan tuhumar da take mu su ba.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel