Ba za mu bari Fayose ya yi takarar shugaban kasa a PDP ba - Makarfi

Ba za mu bari Fayose ya yi takarar shugaban kasa a PDP ba - Makarfi

Shugaban kwamitin rikon-kwarya na babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a takaice Sanata Ahmad Makarfi ya kara jaddada cewa dan arewa ne zai yi takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019 karkashin jam'iyyar.

Sanata Makarfi yayi wannan tsokacin ne a lokacin da ya ke bayana a yayin taron da jigogin jam'iyyar ta PDP daga arewacin kasar nan suka gabatar da taron su a jiya Talata.

Ba za mu bari Fayose ya yi takarar shugaban kasa a PDP ba - Makarfi

Ba za mu bari Fayose ya yi takarar shugaban kasa a PDP ba - Makarfi

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta fara 'maja' da kananan jam'iyyu

NAIJ.com dai ta samu daga bakin shugaban jam'iyyar cewa abunda jam'iyyar ta yanke dai shine yankin kudancin kasar nan zai shugabanci jam'iyyar yayin da kuma yankin arewacin jam'iyyar zai yi takarar shugabancin kasar nan a 2019 kuma a hakan ake har yanzu.

Daga nan ne kuma sai shugaban na jam'iyyar ta PDP ya kara jaddada muhimmancin hadin kai da kuma mutunta juna da kuma manufofi da tsare-tsaren jam'iyyar domin samun nasara a zabukan da ke tafe.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a watan da ya gabata ne dai Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya kaddamar da gangamin yakin neman zaben sa na shugaban kasa a garin Abuja.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taron shugabanin kasashen duniya a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taron shugabanin kasashen duniya a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi
NAIJ.com
Mailfire view pixel