Arewa ba ta jin tsoron sake fasalin kundi tsarin mulkin Najeriya - in ji shugabannin Arewa

Arewa ba ta jin tsoron sake fasalin kundi tsarin mulkin Najeriya - in ji shugabannin Arewa

- Shugabannin sun bayyana cewa yankin arewa ba ta jin tsoron sake fasalin kundi tsarin mulkin kasar

- Shugabannin sun bayyana hakan ne a wani taron kwana biyu a Kaduna

- Shugabannin arewa sun yi la'akari cewa ko da yake arewa ba ta yi matsayi ba a kan batun

Shugabannin siyasa da na addinai a yankin arewacin kasar sun tattauna akan batun sake gyaran tsarin mulkin Najeriya , duk sun amince a kan cewa yankin arewa ba ta jin tsoron sake fasalin kundi tsarin mulkin kasar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, shugabannin arewa sun sanar da wannan matsayi ne a wani taron kwana biyu a kan ‘Arewa da kuma makomar Najeriya' wadda Cibiyar Nazarin Binciken Arewa, ARDP, ta shirya, wanda aka fara a Kaduna a safiyar yau Laraba, 11 ga watan Oktoba.

Gwamna AminiuTambuwal na jihar Sakkwato da Farfesa Ango Abdullahi da Sheik Daihiru Bauchi da kungiyar kristoci ta Najeriya yankin arewa (CAN) da kuma kungiyar Jamaatu Nasir Islam (JNI) sun yi la'akari da cewa ko da yake Arewa ba ta yi matsayi ba a kan batun, amma ba wai tana ji tsoro ba ne.

Arewa ba ta jin tsoron sake fasalin kundi tsarin mulkin Najeriya - in ji shugabannin Arewa

Shugabnnin yankin Arewa

KU KARANTA: Bin kwakwap: Shin ko cikin bayanan Buhari na murnar samun 'yancin kai akwai zuqi-ta malle a ciki?

Sauran kungiyoyi masu halartar taron sune kungiyar dattawan arewa, kungiyar wakilai Arewa, Arewa Consultative Forum, CODE Group, Arewa Reawakening, Jam'iyar Matan Arewa da kuma kungiyoyin matasan arewa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel