Dukkan ilahirin jam'iyyar Labour Party ta jihar Osun za ta koma PDP - Makarfi

Dukkan ilahirin jam'iyyar Labour Party ta jihar Osun za ta koma PDP - Makarfi

Shugaban jam'iyyar PDP Sanata Ahmad Makarfi ya sanar da cewa an kammala dukkan shire-shire a jam'iyyance domin karbar kaf ilahirin jam'iyyar Labour Party ta jihar Osun zuwa babbar jam'iyyar adawar ta Najeriya da yake jagoranta.

Shugaban jam'iyyar ta PDP ya kwarmata wannan zancen ne lokacin da yake jawabi a hedikwatar jam'iyyar dake a Wadata Plaza a babban birnin tarayya Abuja.

Dukkan ilahirin jam'iyyar Labour Party ta jihar Osun za ta koma PDP - Makarfi

Dukkan ilahirin jam'iyyar Labour Party ta jihar Osun za ta koma PDP - Makarfi

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun gabza fada da yan Boko Haram a Gwoza

NAIJ.com haka zalika ta samu cewa tuni jam'iyyar ta PDP a matkin kasa ta gama yanke shawarar cilla damar takarar shugabancin kasa a jam'iyyar zuwa yankin arewacin kasar kuma a hakikanin gaskiya ba zata canza daga hakan ba.

Sanata Makarfi daga nan ne kuma sai ya shawarci dukkan masu son tsayawa takarar shugabancin kasar da suka fito daga kudancin kasar da su hakura su barwa takwarorin su daga arewacin kasar domin samun hadin kan jam'iyyar.

Su ma kuma da suke nasu tsokacin, tsohon shugaban jam'iyyar Dakta Ahmadu Ali ya ja hankalin sauran 'ya'yan jam'iyyar da su zabi mutane nagari don tafiyar da al'amurran jam'iyyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel