Dakarun Amurka da zasu farma Koriya ta Arewa sun fara isa Koriya ta Kudu

Dakarun Amurka da zasu farma Koriya ta Arewa sun fara isa Koriya ta Kudu

Labaran da muke samu da dumi-dumin su na nuni ne da cewa yanzu haka manyan dakarun kasar Amurka sun doshi kasar Koriya ta Kudu domin kafa sansanin jiran ko ta kwana da zummar farwa kasar Koriya ta Arewa dake makwaftaka da ita idan bukatar hakan ta taso.

Ita dai kasar ta Koriya ta Kudu dake makwaftaka da Koriya ta Arewa tana zaman kawa ce ga kasar Amurka da a halin yanzu basa ga-maciji da kasar ta Koriya ta Arewa musamman ma ganin yadda shugaban kasashen biyu suka rika cacar baki tare kuma da nuna junan su da yatsa.

Dakarun Amurka da zasu farma Koriya ta Arewa sun fara isa Koriya ta Kudu

Dakarun Amurka da zasu farma Koriya ta Arewa sun fara isa Koriya ta Kudu

KU KARANTA: Jiga-jigan PDP a Arewa sun watsawa Fayose kasa a ido

NAIJ.com dai ta samu cewa babban makasudin da ya haddasa cece-kuce a tsakanin kasashen biyu shine batun nan na kerawa tare kuma da mallakar makamin Nukiliya da kasar Koriya ta Arewa ta dukufa ta na yi lamarin da bai yiwa kasar ta Amurka dadi ba ita kuma.

Haka zalika a kwanan baya ma dai shugaban kasar na Amurka Donald Trump dai ya sha alwashin ragargazar kasar ta Koriya ta Arewa dake takalar mata hanci da wasu muggan makaman kare dangi da take gwadawa a yan kwanakin nan yayin da shi kuma shugaban kasar na Koriya ta Arewa Kim Un ya ce 'shege-ka-fasa'.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel