Ibe Kachikwu ya bayyana wasiƙarsa don ya kunyata Buhari - Tanko Yakasai

Ibe Kachikwu ya bayyana wasiƙarsa don ya kunyata Buhari - Tanko Yakasai

- Alhaji Tanko Yakasai ya ce ministan albarkatun man fetur ya bayyana wasikarsa don ya kunyata shugaba Buhari

- Yakasai ya bayyana cewa Ibe Kachikwu yana so ya haifar da tunanin cewa shugaba Buhari na da rauni

- Dattijon ya ce wasikar na dauke da jerin matsalolin da suka kasance suna da tsawon lokaci

Alhaji Tanko Yakasai a ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba ya yi ikirarin cewa karamin ministan albarkatun man fetur, Dokta Emmanuel Ibe Kachikwu, ya bayyana wasikar da ya rubuta wa shugaba Muhammadu Buhari don kunyata shugaban.

Har ila yau Yakasai ya yi ikirarin cewa da gangan ne ministan ya bayyanar da wasiƙar ga jama'a domin ya haifar da tunanin cewa shugaba Buhari na da rauni.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, a cikin wata sanarwa da ya sanya hannu, dattijon ya yi ikirarin cewa wasika na Kachikwu ya haifar da tunanin cewa shugaba Buhari bai da masani ga wasu abubuwa.

Ibe Kachikwu ya bayyana wasiƙarsa don ya kunyata Buhari - Tanko Yakasai

Alhaji Tanko Yakasai

Yakasai ya ce, "Daga cikin abin da ministan ya rubuta, yana dauke da jerin matsalolin da suka kasance suna da tsawon lokaci”.

KU KARANTA: Buhari ne ya bani damar aiki da Naira Biliyan 640 yayin da yake kasar Landan - Baru

"Kowa ya san cewa shugaban kasa ya yi fiye da watanni uku ba ya Najeriya, ya kamata ministan ya gabatar irin wannan ga mataimakin shugaban kasa a lokacin da shugaba Buhari ba ya nan".

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel