Sunaye 17 dake nuna alakar kabilancin Buhari da Jonathan wajen nade-nade a kamfanin NNPC

Sunaye 17 dake nuna alakar kabilancin Buhari da Jonathan wajen nade-nade a kamfanin NNPC

A cigaba da korafe-korafe akan yadda ake shugabantar kamfanin man fetur na kasa NNPC, wata kungiya ta na gargadin 'yan Najeriya akan su gujewa yaudarar karamin ministan man fetur Ibe Kachikwu.

Yayin da wannan kungiyar take gargadi, APC ta ture tuhumar da 'yan uba suke yiwa shugaban kasa Buhari akan nuna kabilanci wajen nade-nade, inda ta alakanta gwamnatin shugaban kasa na yanzu da tsohuwar gwamnatin Goodluck.

Kungiyar Accountability Vanguard ta bayyana cewa, yunkurin da kamfanin NNPCda wasu 'yan kasar Najeriya wajen yaudarar ministan abin yin tir da wus ne.

Sunaye 17 da suke nuna alakar kabilanci wajen nade-nade a kamfanin NNPC na lokacin Buhari da Jonathan
Sunaye 17 da suke nuna alakar kabilanci wajen nade-nade a kamfanin NNPC na lokacin Buhari da Jonathan

Baya ga haka, Legit.ng ta fahimci akwai korafe-korafe da suke tasowa dangane da alakar nade-nade wajen shugabantar wannan kamfani na man fetur awato NNPC, ind al'umma da dama suke tuhumar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da nuna kabilanci a wajen nadin.

KARANTA KUMA: Yadda gudanarwar sojin kasa ta dakile ta'addanci a yankin Kudu Maso Gabas - Bincike

Shafin jam'iyyar APC na dandalin sada zumunta na facebook mai sunan APC News TV, ya ruwaito jerin sunayen nade-naden kamfanin NNPC da tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi, inda ta fayyace zare da abawa wajen nuna shin kowace gwamnati ce ta yi kabilaci a wajen nadin shugabannin kamfani.

Ga jerin sunayen shugabannin NNPC a lokacin tsohuwar Gwamnatin Jonathan tare da yankunan da suka fito.

1. Ciyaman na shugabanni, Mrs. Diezani Alison Madueke - Kudu

2. Bukar Abdullahi - Arewa.

3. Steven Orasaya - Kudu

4. Olusegun Okunu - Kudu

5. Daniel Wadzani - Kudu

6. Benard O.N Otti - Kudu.

7. Peter Nmadu - Kudu.

8. Taye Haruna - Kudu

Ga kuma jerin sunayen shugabannin kamfanin a gwamnatin Buhari tare da yankunan da suka fito.

1. Ciyaman na shugabanni, Dr.Ibe Kachikwu - Kudu

2. Kacala M. Baru - Arewa

3. Mahmud Dutse - Arewa

4. Abba Kyari - Arewa

5. Thomas John -Kudu

6. Pius O. Akin - Kudu

7. Tajudeen Umar -- Kudu

8. Lawal Mohammed -Arewa

9. Yusuf Lawal -Arewa

Wannan shaida da jam'iyyar APC ta fitar ta na kokarin kore duk wata tuhuma da ake yiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen kabilaci a nade-naden da yake gudanarwa.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel