Zaben 2019: Jiga-jigan jam'iyyar PDP a arewa sun watsawa Gwamna Fayose kasa a ido

Zaben 2019: Jiga-jigan jam'iyyar PDP a arewa sun watsawa Gwamna Fayose kasa a ido

Jiga-jigan babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a takaice sun yi fatali da kudurin nan na Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose na fitowa takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019 mai zuwa inda suka bukaci da ya daratta hukuncin uwar jam'iyya.

Jiga-jigan jam'iyyar ta PDP da suka tattauna game da lamarin a jiya karkashin jagorancin tsohon minista Farfesa Jerry Gana sun bayyana cewa yankin na arewa da uwar jam'iyyar ta ba damar ya fiddo dan takarar shugaban kasar na da zakakuran da za su iya masu tarin yawa.

Zaben 2019: Jiga-jigan jam'iyyar PDP a arewa sun watsawa Gwamna Fayose kasa a ido

Zaben 2019: Jiga-jigan jam'iyyar PDP a arewa sun watsawa Gwamna Fayose kasa a ido

KU KARANTA: Sanatan Najeriya ya caccaki shugaba Buhari

NAIJ.com ta samu dai cewa shima tsohon shugaban jam'iyyar Dakta Bello Halliru ya bayyana cewa kamata yayi dukkan hukunce hukuncen da uwar jam'iyyar ta bayar ayi biyayya gare su domin samun nasarar kowa da kowa.

Sannan kuma ya kara da cewa: "Shi wannan yarjejeniyar ta bayayya tsakanin bangarorin kasar nan akwai ta har a cikin kundin tsarin mulkin mu."

Wasu daga cikin tsaffin Gwamnonin jam'iyyar da suka halarci taron sun hada da Idris Wada (Kogi), Ramalan Yero (Kaduna), Babangida Aliyu (Niger), Malam Ibrahim Shekarau (Kano) da kuma Ibrahim Shema (Katsina).

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel