Masu garkuwa da mutane sun sako wasu ma’aikata kasar Sin 2 da suka sace a Abuja

Masu garkuwa da mutane sun sako wasu ma’aikata kasar Sin 2 da suka sace a Abuja

- An sako ma'aikatan kamfanin CGECC 2 da masu garkuwa da mutane suka sace a Abuja

- Sai da aka biya makudan kudade kafin aka sako su

An sako ma’aikatan kamfanin gini daga kasar Sin guda 2 da aka sace a lokacin da suke bibiyan aikin gyara titin Abuja.

Tun da aka kama ma’aikatan a ranar 5 ga watan Oktoba babu wanda ya kara ji daga gare su.

Ma’aikata 2 masu suna Hu Kai, da Pan Xiang, wanda suke aiki a kamfanin CGECC, dake Abuja, sun samu yanci daga hanun masu garkuwa da mutane ne a ranar Litinin.

Masu garkuwa da mutane sun sako wasu ma’aikata kasar Sin 2 da suka sace a Abuja

Masu garkuwa da mutane sun sako wasu ma’aikata kasar Sin 2 da suka sace a Abuja

NAIJ.com ta samu rahoton cewa sai da kamfanin ta biya makudan kudade kamfin aka sako ma’aikatan.

KU KARANTA : Wata matar aure ta tona asirin Faston cocin su da ye neme ta a shafin Whatsapp

An ce kokarin da yan sanda suka yi wajen neman ma’aikatan ya sa aka sako su.

Mai magana da yawun hukumar yansanda, Anjugurl Manza ya tabbatar aukuwan wannan lamari, amma yaki fada wa manema labarai ko an biya kudi kafin aka sako ma’aikatan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel