Wata Sabuwa: Yanzunnan gwamnatin tarayya ta hana dukkan likitocinta aiki a asibitocinsu na kudi

Wata Sabuwa: Yanzunnan gwamnatin tarayya ta hana dukkan likitocinta aiki a asibitocinsu na kudi

Dama dai likitoci kan gwammace su nemi kudi a asibitoci na kudi, ko nasu da suka kafa, maimakon su taimakawa alakawa masu zuwa asibitoci na gwamnati, inda likitoci suka yi kadan. Da zarar rana tayi sai a nemi likitoci a rasa, sun tai tasu sabgar.

Wata Sabuwa: Yanzunnan gwamnatin tarayya ta hana dukkan likitocinta aiki a asibitocinsu na kudi

Wata Sabuwa: Yanzunnan gwamnatin tarayya ta hana dukkan likitocinta aiki a asibitocinsu na kudi

A bayan taron majalisar zartaswa da shugaba Buhari ya shugabanta a yau dinnan, gwamnatin ta fitar da sanarwa ga dukkan likitoci da suke aiki a asibitin gwamnati, da kada su sake zuwa aiki a asibitinsu da suka kafa, musamman na kudi, saboda hakan baya cikin tsari, su hada albashi biyu.

Dama dai likitoci, duk da cewa gwamnati ce ta dauki nauyin karatunsu, sannan ta basu aiki da albashi mai tsoka, sukan gwammace su nemi kudi a asibitin kudi, ko kuma su tsallake asibiti a kasashen waje su bar talakka da wahalar neman magani.

DUBA WANNAN: Shin shugaba Buhari ya sharota ne?

A sanarwar da suka fitar, ministan kwadago da na lafiya, a yau dinnan, sun ce daga yanzu, gwamnati ta haramta aiki biyu ga likitoci, dole ne su zauna a asibitin gwamnati da ake basu albashi, su yi aiki har lokacin tashinsu yayi.

Ministocin sun kuma ce, daga yanzu, duk wani mahaluki da ya je yajin aiki, to ya tabbata bashi da albashi ko na sisin kwabo.

Ga dukkan alamu dai wannan aikin Buhari ne, na kokarin kawo lafiya mai araha ga talakka.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel