Kotun ECOWAS ta umarci gwamnatin Najeriya da biyan diyyar dalibin soja da ya mutu a NDA

Kotun ECOWAS ta umarci gwamnatin Najeriya da biyan diyyar dalibin soja da ya mutu a NDA

- An tunkuda yaron a ruwa ba kayan agaji bayan ya ce musu bai iya ruwa ba

- Hukumar sojoji ta ki yin komai a kai

- Mahaifin yaron ya kai gwamnatin Najeriya kara a babbar kotun ECOWAS

Kotun kungiyar cinikayyar nahiyar Afirka ta yamma, ECOWAS, ta umarci gwamnatin Najeriya da ta biya diyyar dala dubu 75,000 (Naira miliyan 27) ga iyalan yaron da ya mutu a sakamakon cin zali a makarantar koyon soja ta Kaduna (NDA).

Kotun ECOWAS ta umarci gwamnatin Najeriya da biyan diyyar dalibin soja da ya mutu a NDA

Kotun ECOWAS ta umarci gwamnatin Najeriya da biyan diyyar dalibin soja da ya mutu a NDA

Yaron sunan sa El-Shadai, dan shekara 19.

Alkalin da ya saurari karar, Justis Friday Nwoke, ya bada wannan umarni ne a ranar Talatar da ta gabata. Ya ce a biya mahaifin yaron da ya shigar da karar, Wing Kwamanda Danladi Agulu-Kwasu (mai ritaya) diyyar.

Mahaifin ya ce an yi wa dan shi sanadiyyar ran sa a lokacin da ake koyan fada a ruwa a ranar 30 ga Afrilu 2015. Ya sanar da kotu cewa an tunkuda yaron ruwa ba kayan agaji bayan ya sanar da su bai iya ruwa ba. Wannan ya faru ne a tafkin Kangima Dama, wanda zurfin shi ya kai mita 100.

Mahaifin ya kara da cewa hukumar NDA da ta sojoji taki daukar wani mataki a kai shi yasa ya shigar da karar kotun ECOWAS.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta hana dukkan likitocinta aiki a asibitocinsu na kudi

Alkalin ya ce saboda wannan keta haddin dan Adam da aka yi, da kuma kin daukar mataki a kai, ya umarci gwamnati da ta biya diyyar yaron, sannan kuma ta bincika ta gano wadanda da hannun su a cikin wannan katobarar don su ma a hukunta su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel