Yarbawa, Hausawa, da Ibo sun shahara wajen cin hanci da rashawa, an gina cocinan Najeriya da kudaden rashawa – Revaren Yomi

Yarbawa, Hausawa, da Ibo sun shahara wajen cin hanci da rashawa, an gina cocinan Najeriya da kudaden rashawa – Revaren Yomi

- Rev Kasali ya ce kusan duka cocinan Najeriya da kudin rashawa aka gina su

- Hausawa sun fi kowace kabila cin hanci da rashawa Najeriya inji fasto Kasali

- Kasali ya ce duk faston da ke son kudi babu Allah a zuciyar sa

Shugaban cocin Truth Ministry dake Legas, Ravaren Yomi Kasali, ya shaida cewa, kusan duka cocinan Najeriya da kudin rashawa aka gina su.

Faston ya ce a lokacin da ake ganin yarbawa suna da cin hanci da rashawa, kabilan Ibo sun fi su, Hausawa kuma sun fi kowa.

Rev, Kasali ya bayyana haka ne lokacin da yake wa’azi a cocin sa, yace fastoci da dama ba su damu da sanin hanyoyin da ake samo kudaden da ake ba su ba.

Yarbawa, Hausawa, da Ibo sun shahara wajen cin hanci da rashawa, a gina cocinan Najeriya da kudaden rashawa ne – Revaren. Yomi

Yarbawa, Hausawa, da Ibo sun shahara wajen cin hanci da rashawa, a gina cocinan Najeriya da kudaden rashawa ne – Revaren. Yomi

Ya fada ma mabiyan sa cewa, duk faston da yake son kudi bai san Allah ba.

KU KARANTA : Wani hadimin Jonathan ya caccaki Atiku Abubakar akan yunkurin dawowa PDP

Kasali ya ce cin hanci da rashawa shine babbar addini yan Najeriya a yanzu.

“Cin hanci da rashawa shine babbar addinin yan Najeriya. Musulmai kashi 48 kristoci kashi 48.

“Yan siyayasan Najeriya ba sa taro sai sunyi adu’a amma babu wanda ya kai su cin hanci da rashawa.

“Sun lalata malaman addini da kudin rashawa. Duk inda kuka ga malamin addini mai son kudi, babu Allah a zuciyar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel