Batun sata a hukumar JAMB, ko dai sharota kawai Kemi Adeosun tayi?

Batun sata a hukumar JAMB, ko dai sharota kawai Kemi Adeosun tayi?

A ranar 13 ga watan Satumbar bana ne dai ministar kudi, Madam Kemi Adeosun, ta ce gwamnatinsu zata binciki tsofin shuwagabannin hukumar JAMB, masu gudanar da jarrabawar shiga jami'a, kan zzargin cin hanci da makale kudaden da suka tara. Bincike na so ya gano meye gaskiyar lamarin.

Batun sata a hukumar JAMB, ko dai sharota kawai Kemi Adeosun tayi?

Batun sata a hukumar JAMB, ko dai sharota kawai Kemi Adeosun tayi?

A cewarta dai, Madam Kemi Adeosun, ministar kudi ta kasa, hukumar JAMB bata taba bada abin da ya haura naira miliyan 3 a shekara ba, a tarihin hukumar na kusan shekaru 40 da kauwa, duk da su suke karbar kudaden jarrabawa daga hannun yara.

Da jaridar Premium Times ta bincika kuwa, sai ta taras, batun nata ba gaskiya bane, shuwagabannin baya suna turo wa gwamnatin tarayya kudi da ya haura miliyan uku na nairori, a wasu shekarun, inda a wasu shekarun kuma, ko sisi basu turowa, kashe abinsu suke yi.

DUBA WANNAN: Shehu Sani na da jaa kan batun ciwo bashi da Buhari zayyi

Sai dai fadinta na cewa a bana ne aka i samun kudi daga hukumar, wannan gaskiya ne, domin hukumar tuni ta turo naira biliyan 5 ga asusun tarayya, maimakon 'yan miliyoyi da a da suke turowa, duk kuwa da cewa ba kudi na jarrabawa gwamnati ta kara ba.

Shugaban hukumar dai, yace bayan biliyan 5 dinma, kafin shekarar nan ta kare, zai kara saka biliyan ukku a asusun gwamnatin tarayya, wanda zai kawo jimillar kudin biliyan 8 a bana kadai.

Lallai shuwagabannin baya na hukumar JAMB na da batun amsawa gaban kuliya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel