Bin kwakwap: Shin ko cikin bayanan Buhari na murnar samun 'yancin kai akwai zuqi-ta malle a ciki?

Bin kwakwap: Shin ko cikin bayanan Buhari na murnar samun 'yancin kai akwai zuqi-ta malle a ciki?

Masharhanta siyasa a Najeriya na bin diddigin wai ko cikin bayanan da shugaba Buhari ya gabatar na murnar cikar Najeriya shekaru 57 da ballewa daga mulukiyar Birtaniya akwai shaci-fadi a ciki, ga dai yadda suka zayyana.

Bin kwakwap: Shin ko cikin bayanan Buhari na murnar samun 'yancin kai akwai zuqi-ta malle a ciki?

Bin kwakwap: Shin ko cikin bayanan Buhari na murnar samun 'yancin kai akwai zuqi-ta malle a ciki?

A batunsa na 'ba'a bar ko sisi ba' bayan fitar da mai kusan ganga miliyan biyu a rana daya, da gwamnatocin PDP suka yi a baya, masu bin kwakwap sunce shugaban sharata kawai yayi, domin wai ya sami makudan daloli a asusun gwamnati, misali:

- A asusun kamfanin gas na NLNG akwai dala biliyan 2 a ajje a lokacin da ya karbi mulki

- A asusun National Sovereign Investment akwai naira biliyan 200 jibge

- Dala biliyan biyu ya taras a asusun rarar man fetur na excess crude

DUBA WANNAN: Shehu Sani yace sai an musu bayanin a inna za'a ciwo bashi kafin su bawa shuagaba Buhari goyon baya

A cewar masu sharhi dai, wannan kudade ne da duk mai gwamnati a hannu ka iya fara kalaci dasu kafin a nemo wasu, don haka ba daidai bane shugaban yayi ta korafin cewa bai sami ko sisi ba a asusun gwamnati, sai dai yace bai samu da yawa ba.

Batunsa kuwa na anyi almubazziranci da sata da almundahana da kudaden da ya kamata ace an adana, wannan gaskiya ne. Ya dai kamata ace abin da ya gada ya ninka hakan kamar sau 100, kamar yadda sauran gwamnatoci kan barwa magadansu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel