Akwai dan majalisar jihar Rivas a cikin mu – Inji wani dan kungiyar asiri

Akwai dan majalisar jihar Rivas a cikin mu – Inji wani dan kungiyar asiri

- Oti ya zargi wani dan majalisar a jihar Rivas da zama dan kungiyar asiri

- Justice Oti mai shekaru 24 ya shahara wajen kisan kai da garkuwa da mutane

- Jam'ian yan sanda sun nemi izinin kakakin majalisar jihar Rivas dan yiwa dan majalisar bincike

Shahararren mai garkuwa da mutane da kisan kai, mai suna Justice Oti wanda aka fi sani da High Tension, ya zargi wani dan majalisar dokoki na jihar Rivas da zama dan kungiyar su na asiri.

An haifi Oti wanda ya kansance daga karamar hukumar gabashin Ahoada a ranar 7 ga watan Mayu na shekarar 1993.

Ya tabbatar wa yan sanda cewa, shi dan kungiyar asirin Iceland ne, kuma ya kashe mutane 15 yan kungiyar da suke hamayya da juna mai suna Greenland Cult.

Akwai dan majalissar jihar Rivas a cikin mu – Inji wani dan kungiyar asiri

Akwai dan majalissar jihar Rivas a cikin mu – Inji wani dan kungiyar asiri

Oti wanda ake zargin sa da yin garkuwa da mutane ya bayyana haka ne a ranar Talata a birnin Fatakol bayan an kama shi.

KU KARANTA : Yan kasuwa sun rufe wata kasuwa a Abuja bisa zargin gwamnati za ta kure su daga kasuwan

Oti wada yake cikin wadanda suka samu rangwame daga gwamnatin Nyseome Wike karkashin ‘Amnesty ‘ da aka yi a shekaran da ta gabata akan ajiye makaman su, ya ce shi bai gama ajiye makaman sa ba.

An kama Oti wanda ake zargin sa da yin garkuwa da mutane a jihar Bauchi, ya ce ya kashe mutane da dama wajen mayar da martani.

Rundunar yansadar jihar Rivas su rubuta wa kakakin majalissar jihar, Ikuiniyi Owaji Lani wasikar neman izinin yi wa dan majalissar da ake zargi bincike.

A cikin wanda aka kama akwai wani dalibin jam’iar Fatakol (UNIPORT) Blessed Francis mai shekaru 22, da laifin fashi da makami.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
INEC ta kori jami'anta 2 akan zargin yi wa gwamnan jihar Kogi rajista so biyu

INEC ta kori jami'anta 2 akan zargin yi wa gwamnan jihar Kogi rajista so biyu

INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu
NAIJ.com
Mailfire view pixel