Gwamantin jihar Benuwe zata tanadar wa makiyaya wuraren kiwo na zamani guda 6

Gwamantin jihar Benuwe zata tanadar wa makiyaya wuraren kiwo na zamani guda 6

- Gwamnatin Jihar Benue zata samar da gidajen gona guda 6 don killece dabbobin da aka kama suna kiwo kara zube

- Zata samar da gonakin ne don tabbatar da dokar hana yawon kiwo kara zube

- Mai bayar da shawara kan harkar tsaro na Jihar ne ya bayar da wannan sanarwa

A ranar Talata ne 10 ga watan Oktoba, Gwamnatin Jihar Benue ta sanar da cewan zata samar da gidan gonaki guda 6 don killace dabbobin da aka kama su na kiwo kara zube. Zata yi hakan ne don tabbatar da dokar hana yawon kiwon kara zube.

Gwamnan Jihar wato Samuel Ortom ne ya sa hannu a takardar dokar a ranar 2 ga watan Mayu don magance hargitsi tsakanin manoma da makiyaya da ya ki ci ya ki cinyewa. NAN ta ruwaito cewan Gwamnan ya ce dokar zata fara aiki ne a 1 ga watan Nuwamba.

Gwamantin jihar Benue zata tanadar wa makiyaya wuraren kiwo na zamani

Gwamantin jihar Benue zata tanadar wa makiyaya wuraren kiwo na zamani

Mai ba wa Gwamnatin Jihar shawara kan harkokin tsaro wato Kwanel Edwin Jando (murabus), shi ne ya sanar da kudirin Gwamnatin na samar da gidan gonakin. Ya ba da sanarwan ne bayan wata zama da suka yi don neman fara aiwatar da dokar.

DUBA WANNAN: Biyafara: An dage sauraron Shari'a tsakanin Nnamdi Kanu da Gwamnatin Tarayya

Ya ce an yi zaman ne don wayar da kan wadanda dokar ta shafa musamman makiyaya. Ya kuma ce gonakin za su zama wurin tsare dabbobin da aka kama suna kiwo kara zube ne a inda bayan kawana 7 za'a yi gwanjon su idan har mai su bai zo ya biya taran da aka yank masa ba.

Za'a samar da gonakin ne a Kwande, Katsina-Ala, Ukum, Guma, Makurdi da kuma tsakanin Gwer ta Yamma da Agatu. Gwamnati ba za ta samarwa makiyaya wurin kiwo. Duk kuma mai bukatar samarwa sai ya bi tsarin da doka ta tanadar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel