Shehu Sani na da jaa, kan batun ciwo uban bashi da Buhari zayyi

Shehu Sani na da jaa, kan batun ciwo uban bashi da Buhari zayyi

- Sanata Shehu Sani dai dan APC ne mai sukar jam'iyyar akai-a kai, shine kuma shugaban kwamitin majalisar kan batun ciwo basussuka

- 'Sai an mana bayanin a ina za'a ciwo bashi kuma yaushe za'a biya sannan zamu amince'

Sanata Shehu Sani ya zanta da gidan rediyon BBC, inda yake bayyana aikin kwamitinsa kan batun ciwo uwan bashi da shugaba Buhari zai sake yi.

Shehu Sani na da jaa, kan batun ciwo uban bashi da Buhari zayyi

Shehu Sani na da jaa, kan batun ciwo uban bashi da Buhari zayyi

A cewar Sanatan mai kokarin kare hakkin talakawa, yace zasu kira Ministar kudi Kemi Adeosun, tazo zauren majalisar domin ta kare gwamnatinsu ta yadda suke niyyar ciwo bashin, me zasu yi dashi, a ina zasu ciwo bashin, kuma wadanne sharudda aka kafa kan bashin.

A fadinsa dai, 'tunda ake cewa sai bayan shekaru 30-50 za'a biya bashin, sai munyi ma 'ya'yanmu da jikoki bayani me muka yi da kudin. domin su ne zasu biya. Abin duk da muka tattara na bayanai daga minista Kemi kuma, zamu saka a rahotonmu mu mika wa babban zauren majalisa.'

DUBA WANNAN: Da bindigogi suka zo dakin jarraraba, bayan bugar da masu sa ido

Shugaba Buhari dai ya rattaba takarda ne ga majalisar domin ta bashi damar sake ciyo bashin biliyoyin daloli don wasu muhimman ayyuka da ya ce ya faro, gabanin zabukan da za'a shiga a karshen badi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel