Diezani ta sake babban asara yayinda kotu ta bayar da umurnin kwace wasu gidaje 56 mallakar ta

Diezani ta sake babban asara yayinda kotu ta bayar da umurnin kwace wasu gidaje 56 mallakar ta

- Wata babban kotun tarayya dake Lagas ta bayar da umurnin kwace wasu gidaje 56 dake mallakar tsohuwar ministar man fetur, Misi Diezani Alison-Madueke

- An rahoto cewa ministar ta mallaki gidajen wadanda ke Lagas da Port Harcourt a tsakanin 2011 da 2013

- An ce kadarorin sun kai kimanin naira biliyan 3

A ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba wata babban kotun tarayya dake Lagas ta bayar da umurnin kwace wasu gidaje 56 dake mallakar tsohuwar ministar man fetur, Misi Diezani Alison-Madueke.

An rahoto cewa ministar ta mallaki gidajen wadanda ke Lagas da Port Harcourt a tsakanin 2011 da 2013 inda ake amfani da gaban a matsayin kamfanoni.

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) tayi ikirarin cewa Diezani ta biya dala 21,982,224 na kadarorin, inda suka kara da cewa ana sa ran cewa kudin na daga cikin kudaden da ake tuhuma akai.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari yana nadin banza a Gwamnatin sa Inji Dino Melaye

Premium Times rahoto cewa kadarorin sun kai kimanin naira biliyan 3.

Hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa tace kadarorin sun hada da gidaje 29 wanda suka hada da mai dakuna hudu guda takwas, dukana uku guda shidda, daukna uku madaidaita guda biyu, gidaje biyu iri guda da kuma gida mai dakuna hudu guda daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel