Shugaba Buhari yana nadin banza a Gwamnatin sa Inji Dino Melaye

Shugaba Buhari yana nadin banza a Gwamnatin sa Inji Dino Melaye

- Sanata Dino Melaye ya soki nade-naden Shugaba Buhari

- A cewar Sanatan an jefa wasu aikin da ya fi karfin su

- Dino Melaye ya nemi Shugaba Buhari yayi wasu sauyi

Wani sanannen Sanata a Najeriya ya soki Shugaban Kasa Buhari yace yana nadin banza a Gwamnatin sa.

Shugaba Buhari yana nadin banza a Gwamnatin sa Inji Dino Melaye

Sanata Dino Melaye ya caccaki Shugaba Buhari

Sanata Dino Melaye na Jihar Kogi yace Shugaban kasa Buhari yayi wasu nade da sam ba su dace ba a mulkin sa. Melaye ya bayyana wannan ne a wata hira da yayi da Jaridar Vanguard. A cewar Sanatan mulkin na-gida ake yi a karkashin Gwamnatin Buhari.

KU KARANTA: Wani tsohon Minista ya bayyana abin da zai sa Buhari ya kara lashe zabe

Melaye ya kara da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya rika bada mukamai da su ka fi karfin masu rike da shi a Gwamnatin na sa saboda sanayya kurum. Sanatan yace babu yadda za ayi makeri yayi aikin manomi komai iyawar sa sa karewa.

Sanatan dai yake cewa iya kyawun mai horaswa iya kyawun 'Yan wasan sa don haka yake ganin ya kamata a sauya wasu Ministocin kasar wanda a halin yanzu Shugaba Buhari ne Ministan man fetur.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel