Wani hadimin Jonathan ya caccaki Atiku Abubakar akan yunkurin dawowa PDP

Wani hadimin Jonathan ya caccaki Atiku Abubakar akan yunkurin dawowa PDP

- Jude Imamwe ya caccaki Atiku akan yunkurin dawowa jam'iyyar PDP

- Imamwe ya kalubalanci Atiku ya fito ya fada wa duniya dalilin da zai sa ya canza sheka

- Gwamantin Najeriya ta umarci hukumar NPA ta yanke duk wata alaka da kamfanin Atiku

Mai ba wa tsohon shugaban kasa Jonathan shawara game da al’amarin da ya sahfi daliban makaranta, Jude Imamgwe, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Atiku Abubakar akan yunkurin canza sheka zuwa jam’iyyar PDP.

A wata sanarwa da Imamwe yayi a ranar Talata, ya kalubalanci Atiku Abubakar ya fito ya fada wa duniya dalilin da zai sa ya canza sheka zuwa PDP.

“Atiku ya fito ya bayyana mutanen Najeriya dalilin da yasa tun farko ya bar jam’iyyar PDP zuwa APC, kuma yanzu yana so yakara dawowa PDP."

Atiku : Hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan ya soki Atiku akan yunkurin canza sheka daga APC zuwa PDP

Atiku : Hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan ya soki Atiku akan yunkurin canza sheka daga APC zuwa PDP

“Dole ya fito ya yi mana bayyani mai gamsar, dan mu fahimci manufar sa na yunkurin dawowa jam'iyyar PDP."

KU KARANTA : Boko Haram : Mun kashe Naira miliyan N400m wajen sayan men fetur din jiragen samar yaki – Rundunar sojin samar Najeriya

“Bayan ya bayyana kan sa, dole ya tabbatar wa yan Najeriya cewa, ba zai kara canza sheka ba ko da bai samu abun da ya ke nema ba.

Bayan haka, gwamnatin Najeriya ta umarci hukumar NPA ta yanke duk wata alaka da kamfanin Atiku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel