Ma su ababen hawa a Kano sun koka da jami'an hukumar KAROTA da 'yan sanda

Ma su ababen hawa a Kano sun koka da jami'an hukumar KAROTA da 'yan sanda

Masu ababen hawa a birnin Kano sun koka da dabi'ar jami'an hukumar 'yan sanda da na KAROTA wadan da suka ce sun addabe su a jihar da karbar na goro da haraji marar dalili.

Wasu ma su ababen hawa a jihar sun koka cewar jami'an biyu a mafi yawan lokuta su ne ke haddasa cunkoso don kawai su tatsi direbobi.

Wasu direbobi biyu; Abdulhadi Usman da Musa yaro, sun bayyana jaridar Daily Trust cewar aiyukan hukumomin biyu shine kama duk wanda ya karya dokar tuki amma ba tsayar da direbobi da bincikar su takardun mota ba, domin hakan aikin hukumar kare hadurra ta kasa ne da kuma jami'an VIO.

Ma su ababen hawa a Kano sun koka da jami'an hukumar KAROTA da 'yan sanda

Ma su ababen hawa a Kano sun koka da jami'an hukumar KAROTA da 'yan sanda

Hakazalika masu kekunan adaidaita sahu ma sun koka da hukumomin. Sun ce a mafi yawan lokuta jami'an na labewa a duk wurin da yake da cunkuson ababen hawa don kawai su samu saukin kakabawa direbobi laifin babu gaira, balle dalili.

DUBA WANNAN: Bayan bugar da masu sa ido da kwaya, Dalibai sun fara zuwa dakin jarrabawa da bindiga - Hukumar WAEC

Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda a Jihar Kano, Magaji Musa Majiya, ya ce suna samun koke-koken direbobi a kan halayyar jami'an 'yan sanda, sannan ya bayyana cewar kofar su a bude take domin karbar koken duk jami'in da ya tsangwami wani direba.

Hakazalika jami'in hulda da jama'a na hukumar KAROTA ya ce ya sabawa doka ga jami'an hukumar su nemi kudi a hannu direba domin muna da kotun tafi da gidanka domin hukunta masu karya dokar tuki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel