'Yan bindiga sun kashe tsohon sakataren Jihar Pilato, Moses Gwom tare da jikkata mutum 12

'Yan bindiga sun kashe tsohon sakataren Jihar Pilato, Moses Gwom tare da jikkata mutum 12

- Wasu yan dadi bindiga sun kashe tsohon sakataren Jihar Pilato, Moses Gwom tare da jikkata mutum 12

- Hukumar 'yan sandan Jihar ne ta bayar da wannan rahoto

- Hukumar ta ce 'yan bindigan sun kai harin ne a ranar Talata da misalin karfe 9 na dare

Hukumar 'yan sandan Jihar Pilato ta ce 'yan bindiga sun kashe Moses Gwam wanda tsohon Sakataren Jihar ne. Mai magana da yawun Hukumar mai suna Terna Tyopev ne ya sanar da Jaridar Premium Times a wata tattaunawa da su ka yi ta wayar tarho.

'Yan bindiga sun kashe tsohon sakataren Jihar Pilato, Moses Gwom tare da jikkata mutum 12

'Yan bindiga sun kashe tsohon sakataren Jihar Pilato, Moses Gwom tare da jikkata mutum 12

Tyopev ya ce maharan sun kuma jikkata mutum 12 a harin da suka kai gidan Gwom da ke Barkin Ladi, na daura da Shingen STF, da misalin karfe 9 na dare a ranar Talata.

DUBA WANNAN: Zaben 2019: Atiku ya fara kamfe a yankin Kudu maso Gabas

Mazauna yankin wadanda abun ya faru a idon su sun ce maharan sun far wa jamj'an tsaron shingen STF din ne kafin su fara barin wuta a gidan Gwom.

Tyopev ya ce ya zuwa yanzun dai babu wanda aka kama cikin maharan amma dai ana nan ana bin sahun su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel