Biyafara: An dage sauraron Shari'a tsakanin Nnamdi Kanu da Gwamnatin Tarayya

Biyafara: An dage sauraron Shari'a tsakanin Nnamdi Kanu da Gwamnatin Tarayya

- An dage Karar da Nnamdi Kanu ya shigar kan Gwamnatin Tarayyya sakamakon rashin bayyanar babban lauya mai wakiltan Gwamnatin Najeriya

- A karar da lauyan Kanu ya shigar, ya nemi Gwamnatin Najeriya ta biya shi diyyar miliyan 800 na dalar Amurka

- Lauya ya kuma ce Rundunar Soji da Gwamnatin Najeriya ne kadai su ka san inda Kanu ya ke

An dage sauraron Karar da Shugaban IPOB wato Nnamdi Kanu ya gabatar ga Kungiyar Kasashen Afirika ta Yamma wato ECOWAS, kan take hakkokin sa da Gwamnatin Tarayya ta yi. An dage sauraron karan ne sakamakon rashin bayyanar babban lauya mai wakiltar Gwamnatin Najeria a zauren shari'ar.

An dakatar da sauraran karar gwamnatin tarayya da Nnamdi Kanu ya shigar

An dakatar da sauraran karar gwamnatin tarayya da Nnamdi Kanu ya shigar

An sanar da kotun cewa lauyan mai suna Mista Dayo Apata ya shiga ganawa da mataimakin Shugaban kasa, Osinbajo, lokacin sauraron karar. Abubakar Abdullahi wanda ya wakilci Shugaban Alkalai na Najeriya, shi ne ya nemi a dage sauraron karar zuwa wata rana ta dabam a inda ya ce takardun da suka danganci shari'ar suna hannun Mista Apata.

DUBA WANNAN: Zaben 2019: A shirye muke mu sadaukar ran mu domin PDP tayi nasara - Gwamna Wike

Kanu ya shigar da karar ne kotun ECOWAS ta hannun lauyan sa mai suna Mista Ifeanyi Ojiofor, yana me neman Gwamnatin Najeriya ta biya shi diyyar miliyan 800 na dalar Amurka. Ojiofor a game da dage shari'ar ya ce da gangan Gwamnatin Najeriya ta kawo tsaiko. A nan ne kuma ya nemi ta biya diyyar naira miliyan 2 don wannan jinkiri.

Da manema labarai suka tambayi Ojiofor dalilin rashin bayyanar Kanu a zauren shari'ar sai ya ce Rundunar Soji da Gwamnatin Najeriya kadai suka san inda Kanu ya ke. Ya ce za su bi diddigin inda Kanu ya ke a kotun.

A halin yanzun dai kotun ta dage sauraron karar har zuwa 21 ga watan Nuwamba na wannan shekara.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel