Yan bindiga sun hallaka tsohon Sakataren gwamnatin jihar Filato

Yan bindiga sun hallaka tsohon Sakataren gwamnatin jihar Filato

Kwanan tsohon sakataren gwamnatin jihar Filato, Moses Gwom sun cika, yayin da wasu Yan bindiga suka kai masa hari a kusa da gidansa inda suka hallaka shi, inji rahoton Daily Trust.

Yan bindiga sun cimma Moses ne a karamar hukumar Barikin Ladi, na jihar Filato inda suka kashe shi tare da Soja da kuma wani mai tsaron shago, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

KU KARANTA: Ilimi ya shiga mawuyacin hali a jihar Kaduna: Kalli jarabawar da Malaman firamari suka gagara masawa

Wannan hari ya biyo bayan wani hari da aka kai kimanin sati biyu kenan a garin Kanam, inda wasu yan bindiga suka kashe dakacin kauyen Gyangyang.

Yan bindiga sun hallaka tsohon Sakataren gwamnatin jihar Filato

Yan bindiga

Shugaban rundunar Sojoji na musamman dake jihar Filato, Birgediya Mohammed Bello ya tabbatar a faruwar lamarin, sa’annan ya shaida ma majiyar mu ta wayar tarho cewa maharani sun kashe wani Soja dake zaune a cikin wani shago, da kuma mai tsaron shagon.

“Hakazalika sun harbe wasu Sojoji guda biyu yayin da suke kokarin guduwa, amma a yanzu haka an duba su a Asibitin mu don ganin sun farfado.” Inji Bello.

Shima a nasa bayanin, Kaakakin rundunar yansandan jihar Filato, ASP Tyopev Terna ya tabbatar da harin, inda yace an kai harin ne da misalin karfe 9:20 na dare.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Matattarar barayin mutane a jihar Legas:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel