Boko Haram : Mun kashe Naira miliyan N400m wajen sayan men fetur din jiragen samar yaki – Rundunar sojin samar Najeriya

Boko Haram : Mun kashe Naira miliyan N400m wajen sayan men fetur din jiragen samar yaki – Rundunar sojin samar Najeriya

- NAF ta bayyana kudaden da ta kashe wajen sayar man fetur din jrgin samar yaki

- Rundunar sojin samar Najeriya (NAF) su kashe naira miliyan N400 wajen sayar man fetur

- A cikin watanni 3 jirgin NAF yayi aikin da ya dauki sa’o’i 1,551 da mintina 39

Rundunar sojin samar Najeriya (NAF) su bayyana cewa, sun kashe naira miliyan N400 wajen sayar man fetur din jirgin samar yaki da ake kai yankin Arewa maso Gabas dan yakar yan ta’adan kungiyar Boko Haram tsakanin watan Yuli da Satumba na shekara 2017.

Kwamandan sojin sama na attisayen ‘Operatin Lafiya Dole’ Air Kwamado Tajudeen Yusuf, ya bayyana haka ne a Maiduguri babban birnin Borno, a lokacin da yake zantawa da manema labaru game da kalubale da nasarorin da rudunar ta samu.

Boko Haram : Mun kashe Naira miliyan N400m wajen sayan men fetur din jiragen samar yaki – Rudunar sojin samar Najeriya

Boko Haram : Mun kashe Naira miliyan N400m wajen sayan men fetur din jiragen samar yaki – Rudunar sojin samar Najeriya

A jawabin da yayi, ya ce “Jirgin yakin NAF yayi aikin sa’o’I 1,551 da mintina 39 a cikin watanni uku.

KU KARANTA : Yadda kyamaran CCTV ya kama wai mutum yana sata a Ikeja

Yusuf yace ayyukan rudunar soji sama ya karu sosai wanda ya kunshi taimakawa rundunar sojin kasa.

“Tsakanin, watan Yuli da Satumba na shekara 2017, Jirgin NAF ya kai hare sama da 842 wanda ya dauki sa’o’I 1,551 da mintina 39.

“Jirgin yakin NAF kirar Jet-A1 ya sha mai da ya kai kimanin Lita miliyan 1,596,165 wanda farashin ya sa ya kai miliyan N399,041,250” Inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel